Kin Biyan ‘yan Kwangila Ya Dakatar Da Ciyar Da Ɗalibai a Zamfara
Rashin biyan basussuka ga ‘yan kwangila yayi sanadin dakatar da shirin nan na ciyar da dalibai a makarantun Zamfara.
Dakatar da shirin ciyar da dalibai a daukacin makarantun gwamnati a Zamfara na ci gaba da yin illa ga Daliban makarantu a fadin jihar.
Yayin da aka shiga mako na bakwai da komawa makarantu a Zamfara, har yanzu ba a fara ciyar da daliban ba, sakamakon cewa har yanzu ‘yan kwangilar da ke kawo kayan abincin ba’a biya su kudadensu ba a wa’adin karshe na zangon karatu da aka fita (Last term).
Wani shugaban wata makarantar jeka-ka-dawo da ke Gusau da bai so a ambaci sunansa ba, ya ce dalibai da dama sun daina zuwa makarantar saboda gazawar gwamnati wurin fara aikin ciyar da dalibai abinci.
Ciyarwa ta zama wata al’ada a cikin harkar karatunmu da ake amfani da ita wajen jawo hankalin dalibai zuwa makaranta, sanadiyar dakatarda ciyarwa yassa yanzu dalibai sun daina zuwa makarantar, inji shi.
Shugaban makarantar ya kara da cewa, halin ma yafi muni a makarantun da ke yankunan karkara saboda rahoton da muke samu shi ne, al’ummomin karkara, musamman wadanda ‘yan fashi da makami suka shafa sun hana ‘ya’yansu zuwa makarantar saboda ba su da kudin da zasu baiwa yaransu na abinci.
Da aka tuntubi jami’an hukumar ciyar da abinci ta jihar Zamfara da suka zanta da manema labarai sun tabbatar da cewa har yanzu hukumar ba ta sasanta basussuka tsakaninta da ‘yan kwangilarta ba, wanda hakan yassa hukumar ciyar da daliban jihar ba ta ci gaba da shirinta na ciyar da dalibai a jihar ba.
Sun ce, a iyakar saninsu, Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya rattafa hannu ga takardar biyan basussukan, amma ba su san abin da ke kawo tsaiko daga ma’aikatar kudi ba tun da Gwamna ya bayar da umarnin biyan.
Ya kuma ce, har yanzu hukumar ba ta sasanta kudaden da ake biyarta ba na jami’an ciyar da abinci (Feeding Officers) a tsawon wa’adin da ya gabata inda ya ce matakin ya sa jami’in ciyar da abinci jan baya wajen neman ‘yan kwangilar su ci gaba da samar da abinci akan bashi.
A matakin ma’aikatar kudi ta jihar, wata majiya ta tabbatar wa manema labarai cewa sun karbi takardar biyan bashin, sai dai gwamnan bai bayar da wani karin umarni ba na a saki kudaden ga hukumar ta ciyar da abinci ba.
