Katin Zaɓe Na Dindindin: INEC Na Kira Ga Jama’a Da Su Karɓi Katin Su.
Daga Auwal Isah
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ka ƙasa wato INEC reshen jihar Katsina ta ce, ta kamala buga katunan zaɓen dindindin na mutanen da suka yi rijistar katin a rubu’in shekara na farko dana biyu, amsa kawai ta rage.
Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen ilimantar da masu zabe da hulɗa da jama’a Shehu Sa’idu ya sanya ma hannu.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, katunan yanzu haka suna ofisoshin hukumar zaɓen na ƙananan hukumomi da mazaɓun yankunan da masu katunan suka yi rijistar.
Saidai hukumar zaɓen ta buƙaci waɗanda suke da matsalar sauyin bayanan katunan zaɓe, da wanda nasu ya lalace, da wanda suka sauya wurin zama, da kuma wanda nasu ya ɓace da suyi haƙuri saboda hukumar na aiki tuƙuru don ganin ta kammala masu katunansu.
Hukumar ta kuma buƙaci waɗanda suka cika shekaru 18 da haihuwa, da waɗanda suka cancanci mallakar katin, da suyi rijistar samun katin duba da ana cikin rubu’in shekara na hudu dana ƙarshe na yin rijistar samun katin.
Sanarwar daganan sai ta ce, za a rufe yin rijistar samun katin a ranar 30 ga watan Yunin wannan shekarar ta 2022.
