Jigawa: An gurfanar da matashin da ke guduwa da rufi da ƙofofin masallatai a Jigawa
A yau Alhamis ne a ka gurfanar da Abba Haruna, ɗan shekara 21 da ke damfarar masallatai, sai ya yaye rufi da kuma cire kofofin masallaci ya gudu da su ya sayar.
Tun da fari, dubun Haruna ta cika ne bayan ya yaudari mutanen ƙauyen Konake a garin Kiyawa, Jihar Jigawa cewa larabawa ne su ka bashi kwangilar gyara babban masallacin ƙauyen.
Da ga bisani ne ya sanya a ka cire rufin kwanon masallacin da kuma kofofin, inda ya ranta a na kare.
Sai dai kuma tuni dubunsa ta cika bayan da ƴan sanda su ka kafa masa tarko, su ka kuma samu nasarar cafke shi a Jigawa.
Tuni dai a ka gurfanar da mai laifin a kotun Majistare ta gurfanar da shi a yau a Jigawa, inda mai gabatar da kara ya ce a na zargin shi da zamba, sata da almundahana.
Wakilin mai unguwar Konake, Ussaini Wanzam Ilyasu, ya ce mako biyu da suka gabata ne matashin ya je garin nasu, ind ya ce wata ƙungiya daga ƙasar Larabawa za ta gina musu sabon masallaci, saboda haka za a rushe tsohon.
“Bayan an rushe wani ɓangare na masallacin sai ya ce ciko za a yi da shi, sannan ya zuba ƙofofi da tagogi da kwano da famfon tuƙa-tuƙa a mota suka tafi da su,” a cewar wakilin mai unguwa.
Ya ƙara da cewa matashin ne da kansa ya biya ma’aikatan da suka yi aikin rushe masallacin. “Masu cire kwano aka ba su 5,000, su ma masu cire wayarin aka ba su 2,000. Masu bige haraba ma an ba su 5,000.”
