An Kaddamar Da Fara Ginin Wurin Dindindin Na Hukumar KTSTA Dake Dandagoro, A Jihar Katsina.
An Kaddamar Da Fara Ginin Wurin Dindindin Na Hukumar KTSTA Dake Dandagoro, A Jihar Katsina.
An bada kwangilar aikin ne ga Muntasrab Global Concept Company Limited akan kudi naira ₦20,282,775.91.
Kamar yadda shugaban hukumar KTSTA Haruna Musa Rugoji ya bayyana, aikin ya ƙunshi ruguje tsohuwar kangar harabar, share filin da kuma gina wata katanga.
Ya yi kira ga ɗan kwangilar da ya fidda kwata mai kyau, tare da bada tazara tsakanin bangwon hukumar da gidajen da hukumar ke makwaftaka da ita, inji Popular News Hausa.
A tsokacin shi, wakilin Kamfanin Umar Faruq Musa ya yi alkawarin yin ingantaccen aiki a wurin.
