Jami’an ‘Ƴan Sanda Sun Damƙe Shahararren Ɗan Bindiga A Zamfara
Rundunar ‘yan sandan jihar zamfara ta tabbatar da kama wani ɗan bindiga da yayi ƙaurin suna wajen satar shanu, garkuwa da mutane da kuma sauran miyagun laifuka a yankunan Shinkafi, Zurmi, da kuma Birnin Magaji a jihar zamfara.
Ɗan bindigar mai suna Sani Mati, wanda aka fi sani da mai ‘yan mata, an kama shi da bindigar Ak47, tarin albarusai, da kuma mashin ƙirar Boxer da yake amfani dashi wajen kai hare-hare.
Kakakin rundunar ƴan sandan jahar ta Zamfara, Ayuba El-khana shi ne ya tabbatar da aukuwar lamarin, a yayin wani taron manema labarai da rundunar ta kira da yammacin ranar laraba.
Ayuba El-khana ya ƙara da cewa rundunarsa ta samu wasu bayanan sirri ne da suka taimaka wajen damƙe Sani Mati a kan hanyar zurmi inda yayi yunƙurin tare hanya shi da yaransa domin yin garkuwa da mutane, sai tayi amfani da ƙwararrun dakarunta wajen chafke ɗan bindigar.
A ƙarshe El-khana ya ce wanda aka kama ɗin yana kan amsa tambayoyi da zasu taimaka wajen chafke ƙarin wasu ƴan ta’addar, kafin daga bisani a gurfanar dashi gaban kotu domin yanke masa hukunci.
