Hukumar Zaɓe A Jihar Katsina Ta Tunatar Da Jam’iyyun Siyasa Su Bi Tsare-Tsarenta Gabanin Zaɓen Ƙananan Hukumomin.
Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Katsina ta tunatar da dukkan jam’iyyun siyasa a jihar da suka nuna sha’awar shiga zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi na ranar 15 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa da su tabbatar da ganin sun bi dukkan tsare-tsaren da hukumar ta basu.
Bayanin hakan ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Shehu Sarki Idris ya fitar.
Kamar yadda sanarwar ta ce a cikin tsare-tsaren da aka basu, an bada kwanaki 60 ga dukkan jam’iyyun siyasa su gudanar da zaɓen fidda don fito da yan takardarsu.
Sanarwar ta ƙara da cewa an bayyana wa’adin da za a fara daga ranar 20 ga watan Maris zuwa 20 ga watan Mayun shekarar 2024.
Sanarwar ta ce gudanar da zaɓen fidda gwanin na jam’iyun siyasar ya yi daidai da sashe na 84 ƙaramin sashe na 1 na dokar zaɓe ta shekarar 2022 da aka yima gyaran fuska.
- Haka kuma sanarwar ta ce ya zama wajibi kowace jam’iyar siyasa ta bada wa’adin kwanaki 21 ga hukumar kafin gudanar da aikace-aikacenta, kuma ya kamata a gudanar da zaɓen fidda gwanin daidai da tanade-tanaden jami’yar.
