September 16, 2026

Hukumar Kare Hakkin Bil’adama Ta Yi Allahwadai Da Rushe Gine-gine A Abuja.

0

Hukumar kare hakkin bil’adama da sauran al’ummar Najeriya na ci gaba da yin Allahwadai da rushe-rushen gine-ginen da hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja ke yi.

Ta ce wannan matakin ya wuce gona da iri da hukumar ta ɗauka.

Saboda haka hukumar ta ce, akwai bukatar a samar da matsugunni ga mutanen da abun ya rutsa da su.

Wata mata da abun ya rutsa da ita kuma majiyar Popular News Hausa ta gidan radiyon DW ta zanta ta bayyana cewa, ” an rushe masu gida, basu da sauran wurin kwana.”

Mrs. Grace Bala ta ce, ” na yi kuka da hawaye saboda bamu da kudin sayen wani filin ginawa, ga kuma ruwan sama ana ta yi yanzu.”

Wannan dalilin ne ya sanya kungiyar kare hakkin bil’adama ta duniya shiga cikin lamarin, tare da bayyana cewa abun ya saba ma ka’ida.

Malam Aminu Hayatu ya ce, ” idan mutane sun wace shekaru 50 zaune a wuri, to sun zama yan kasa. Ya ce, idan kuma za a yi amfani da wurin don amfanin al’umma, to dole ne a samar masu da wuri mai kyau da ya cika dukkan sharuddan kare lafiya da hakkin dan adam.

Wasu magidanta dai sun ce, suna zaune wurin ne sama da shekaru 50, wato tun kafin asan za a yi babban birnin tarayya Abuja.

Hukumar ta ce, amma hakan take hakkin dan adam ne.

Hukumar kula da birnin tarayyar Abujar ta ce, ana rushe wuraren ne bisa zargin yan ta’adda da sauran bata-gari na fakewa ne.

Mataimakin ministan Abujar akan aiwatar da ayyuka da sanya ido Ikaro Attah ya ce, sun ta samun rohoton cewa zauna gari banza da sauran yan ta’adda na kai hari akan manyan mutane dama talakawa dake wuraren, dalilin da ya sanya su ɗaukar wannan matakin.

Saidai hukumar kare hakkin bil’adamar ta ce, wannan ba hujja bace, kamata ya yi a kamo masu laifin, tare da gurfanar da su gaban kuliya don tabbatar masu da laifin su.

Hukumar kula da Abujar dai ta ce, ta rushe gine-gine sama da 400. Abunda ta daɗe tana yi kuma babu alamun bari.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *