September 16, 2026

Ƴan Bindiga Sun Kashe Ƴan Sanda Biyu A Katsina

0

Ƴan Bindiga Sun Kashe Ƴan Sanda Biyu A Katsina

‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Ƴan Sanda Biyu Da Kashe Ƴan Bindiga Biyu Har Lahira A Wani Ba Ta Kashi Tsakanin Ƴan Bindiga Da Jami’an Yan Sanda A Dajin Baure Dake Cikin Karamar Hukumar Safana Ta Jihar Katsina.

Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar Katsina, Alhaji Sanusi Buba Ya Bayyana Wa Manema Labarai Ciki Har Da popular News Hausa A Helkwatar Rundunar Ƴan Sandan Jihar Katsina, Dake Hanyar Daura Cikin Garin Katsina Yau Juma’a.

Alhaji Sanusi Buba Ya Kara Da Cewa A Koƙarin Da Muke Na Ganin Mun Kawo Karshen Yan Bindiga, Ariya Kwamanda Na Dutsin-ma, ACP Aminu Umar Ya Jagoranci Wata Tawagar Jami’an Tsaro Zuwa Mabuyar Yan Bindiga A Dajin Baure Dake Karamar Hukumar Safana, Inda Muka Yi Gumurzu Da Su, Inda Muka Yi Nasarar Kakkabe Mabuyar Ta Su Har Muka Kashe Biyu Daga Cikinsu Kuma Mun Samu Bindiga Daya Kirar Ak 47 Da Harsasai 35.

Bayan Haka Ina Jimamin Sanar Da Ku Cewa Ƴan Bindiga Sun Kashe Mana Jajirtattun Ƴan Sanda Biyu, Akwai ASP Yakubu Joshua Mai Lamba AP. No. 151332 Dake Rundunar Ƴan Sandan Ko Ta Kwana Ta 27 Kuma Mai Baiwa Ƴan Sanda Horo Ne Da Kuma Direban Motar Mu Mai Sulke Watau (APC) Sajen Zaharadeen Yuguda Dake Aiki A Karamar Hukumar Safana.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *