Gwamnatin Najeriya Na Shirin Kara Harajin 5% Akan Kira, Aika Sako Da Kuma Damen Hawa Yanar Gizo.
Akwai bukatar masu amfani da layukan sadarwa a Najeriya su kara matsa lamba a cikin kwanaki masu zuwa, yayin da gwamnatin tarayya ta kammala shirin sanya harajin kashi 5% cikin 100% akan kiran waya, sakon katta kwana da kuma amfani da damen hawa yanar gizo.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da manyan masu ruwa da tsaki a fannin da suka hada da kungiyar masu gudanar da harkokin sadarwa ta Najeriya ALTON, kungiyar kamfanonin sadarwa ta Najeriya ATCON da kuma kungiyar NATCOMS, suka nuna rashin amincewarsu da matakin, inda suka bayyana hakan a matsayin sabawa doka, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard.
Sun bayyana matsayinsu ne a Abuja a lokacin taron masu ruwa da tsaki da Hukumar Sadarwa ta Najeriya ta NCC ta shirya kan shirin aiwatar da harajin sadarwa a Najeriya.
Masu ruwa da tsakin dai sun yi nuni da cewa, sanya harajin zai kara dagula wa talakawan Najeriya radadin halin kunci da talauci da suke ciki.
Sabon harajin na kaso 5 cikin 100 na daga cikin sabuwar dokar kudi da shugaban kasa ya sanya wa hannu a shekarar 2020.
Hukumar Kwastam ta Najeriya ce za ta karbo harajin, bisa umarnin shugaban kasa Mohammadu Buhari na cewa ta aiwatar da doka a kan dukkan kamfanonin sadarwa na cikin kasa da wajenta.
A nata jawabin, ministar kudin Najeriya Zainab Ahmed, ta bukaci masu ruwa da tsaki da su bayar da goyon baya wajen aiwatar da harajin kashi 5% cikin 100, inda ta ce an sanar da hakan ne sakamakon raguwar kudaden shigar da gwamnatin tarayya ke samu daga man fetur da iskar gas.
Zainab, wacce ta samu wakilcin mataimakin daraktan haraji da tsare-tsare, Musa Umar, ta yaba wa hukumar ta NCC bisa bayar da damar yin mu’amala da masu ruwa da tsaki da kuma maraba da abubuwan da suka taimaka wajen samar da kudaden shiga.
Ta yi nuni da cewa, kasashen Afirka kamar su Malawi, Uganda, Tanzania da sauransu, duk sun taka rawar gani wurin samar da kudaden shiga.
Tun da farko a jawabinsa na maraba, shugaban hukumar NCC Farfesa Umar Danbatta, ya ce taron ya zama dole domin masu ruwa da tsaki su samu karin haske kan harajin kaso na 5% cikin 100 na ayyukan sadarwar.
Ya ce, “a matsayin hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya, hukumar sadarwa ta Najeriya ta hada hannu da ma’aikatar kudi ta tarayya, hukumar kwastam ta Najeriya da kuma masu ba da shawara daga bankin duniya domin samun cikakkun bayanai.”
A nasa jawabin, Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Najeriya Hameed Ali mai ritaya, ya roki masu ruwa da tsaki da su kasance masu kishin kasa tare da fahimtar gwamnati wajen aiwatar da harajin.
A nasa martanin shugaban kungiyar kamfanonin sadarwa ta Najeriya ALTON, Gbenga Adebayo, ya bayyana sabon tsarin harajin a matsayin wani bakon al’amari da ba a saba gani ba a cikin haraji daban-daban guda 39 da kamfanonin sadarwa ke biya a kasar.
