Gwamnatin Katsina Zata Haɗa Gwiwa Da Ƙasar Marocco Don Farfaɗo Da Noman Auduga – Dikko Raɗɗa
Gwamnatin Katsina Zata Haɗa Gwiwa Da Ƙasar Marocco Don Farfaɗo Da Noman Auduga – Dikko Raɗɗa
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bada tabbacin cewa gwamnatin da ƙasar Marocco zasu yi haɗin gwiwa wajen farfaɗo da noman Auduga a jihar Katsina.
Malam Dikko Raɗɗa Ya bayyana haka a lokacin kaddamar da fara aikin tagwayen hanyoyi da suka ratsa cikin garin Funtua a wani mataki kudirin gwamantin sa bunƙasa birni.
Gwamnan wanda ya ce ya ziyarci ƙasar Marocco ne domin tattaunawa da masana akan batun noman Auduga da ya ce yankin na Funtua ya yi fice a lokutan baya.
“Zamu farfaɗo da noman auduga wanda aka san Nijeriya da shi, kuma yankin Funtua ya yi fice wannan wajen sana’a ” inji shi
Ya ƙara da cewa sun tattauna da wasu kamfanoni da kasar Maroco domin samar da ingantaccen irin auduga da takin zamani da zai bunƙasa noman ta matasa su samu arziki a jihar Katsina baƙi ɗaya.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya kuma jadadda kudirin gwamnatin sa na ganin ya bunƙasa birane wanda ya ce yanzu haka an bada aikin gyaran tagwayen hanyoyin cikin garin Funtua akan kuɗi fiye da Naira biliyan 20.
kazalika ya ƙara da cewa ko shakka babu wannan aiki zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da hulɗar kasuwanci musamman a cikin garin Funtua.
Gwamna Dikko Raɗɗa yana mai cewa an bada wannan aiki ga kamfanin Mother Cat wanda ake sa ran kammalawa cikin watanni 18 idan Allah ya amince.
