September 18, 2026

Gwamnatin Katsina Ta Nemi Muƙadashin Kwantirolan Kwastom Na Ƙasa Ya Ɗauki Mataki Akan Jami’ansu.

0

Gwamnatin jihar Katsina ta koka da yadda wasu jami’an hukumar Customs ke saɓa doka a lokacin da suke aiki a jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Katsina Faruk Lawal Jobe ya bayyana hakan a lokacin da ya amshi bakuncin mukaddashin kwantirolan hukumar na ƙasa Bashir Adewale Adeniyi a ofishinshi.

Faruk Jobe ya ce akwai abubuwan da jami’an hukumar Customs ke aikatawa da suka haɗa dana taho mu game da kuma harbe-harbe akan mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Mataimakin gwamnan ya tunaso yadda jami’an hukumar Customs suka rutsa da shi akan hanyar Jibia kimanin shekaru 5 da suka gabata, inda kuma har yanzu babu wani mataki da aka ɗauka.

Mataimakin gwamnan ya ƙara da bada misalan cewa, kwamishinoni 2, da kuma shugaban ma’aikata na gidan gwamnati sun faɗa komar irin wannan jami’ai na Customs.

Faruk Lawal Ya bayyana damuwa akan irin wannan ayyukan saɓa dokar aiki da jami’an na Customs ke yi.

Ya yi kira ga mukaddashin kwantirolan hukumar na kasa ya binciki wannan muggan ayyukan a tsanake, tare da magance su don guje ma karya doka da oda.

Tunda farko, saidai mukaddashin kwantirolan Bashir Adewale Adeniyi ya ce ya zo jihar Katsina ne domin ya tabbata da ganin an rufe iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar sakamakon abubuwan da ke faruwa a makwabciyar kasar.

Bashir Adewale ya ce, rufe iyar da dukkan kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS masu makwabtaka da ƙasar ta Nijar suka yi shawarar bai-daya ce da aka cimmawa.

Ya kuma ce za a gudanar da bincike dalla dalla akan jami’an Customs ɗin da suka aika laifukan da aka ambata a baya domin hukunta su.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *