Gwamnatin APC Ta Yi Mani Fashin Kuri’u A Jihohi Biyar A Zaɓen 2019 – Atiku Abubakar
Daga El-Zaharadeen Umar
Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyar PDP a zaɓe mai zuwa kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa a shekarar 2019 shi ne ya cinye baban zaɓe da aka yi amma gwamnatin APC ta yi masa kwace da rana tsaka.
Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci shalkwatar jami’yyar PDP da ke Katsina domin ganawa da masu zaɓan fidda gwani (Delegates) dangane da zaɓan da zai gudana nan ba da jimawa ba.
Ɗan takarar wanda ya ce gwamnatin APC ta shirya wani maguɗi da manaƙisa wanda ya yi sanadiyar rashin nasarar sa a wancan zaban.
“Ni na ci zaɓe a jihohin Katsina da Kano da Yobe da Barno da kuma Kaduna amma aka shirya mani cuta a waɗannan wurare.” In ji shi
Ya ƙara da cewa Jami’yyar APC ta kawo rashin haɗin kai a Najeriya, saboda irin banbance banbancen da take nunawa wajan shugabanci, ya ce ya yi alƙawarin idan ya samu nasara babu wani ɓangare da za a sake nunawa banbanci a wannan ƙasar.
Alhaji Atiku Abubakar yana mai cewa zai yi iyakar ƙoƙarinsa wajan haɗa kan ƙasar nan ta zama abu guda, domin zaman lafiya da ƙaruwar arziki.
Haka kuma ɗan takarar ya yi alƙawarin zai dawo da zaman lafiyar da aka rasa a ƙarƙashin mulkin APC, ya ce abinda ‘yan ta’adda suke yi a wannan gwamnatin ba za su yi shi a gwamnatin sa ba.
Atiku Abubakar ya ce babu inda ɗan ta’adda zai ɓoye a daji ba tare da an gano shi ba, da haka za a samu tsaro a bunƙasa tattalin arziki ƙasa.
