November 18, 2026

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kashe Naira Miliyan 50 Wajen Gyara Motocin ‘Yan Sanda 15.

0

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kashe Naira Miliyan 50 Wajen Gyara Motocin ‘Yan Sanda 15.

Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta ƙashe kuɗi har naira miliyan 50 domin gyara motocin ‘yan sanda goma sha biyar da suka lalace don karfafa masu gwiwar yaƙi da ‘yan ta’adda.

Shugaban ma’aikatan ofishin mataimakin gwamnan jihar Katsina Malam Mukhatr Aliyu Saulawa ya bayyana haka a lokacin da yake miƙa motocin ga rundunar ‘yan Sanda a Katsina

Ya ƙara da ce gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ne ya amince da kashe waɗannan kuɗaɗen domin aiwatar da gyaran motocin.

“Wannan aiki na gyaran waɗannan motoci ya biyo bayan rokon da rundunar ‘yan sandan ta yi ta hanyar Kwamishinonan ‘yan sanda na jihar Katsina Aliyu Musa wanda ya yi rokon gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya taimaka masu” inji shi

 

Ya kuma bayyana cewa sun gayyato Kanikawa da masu tada komaɗar mota (pennel beaters) daga makarantar koyon sana’o’i ta Katsina Youth Craft Village domin karfafa masu gwiwa akan sana’ar su.

Shima da yake amsar motocin a madadin shugaban yan sandan Nijeriya da kuma Kwamishina, mataimakin Kwamishinan ‘ya. Sanda DC Ibrahim Sa’ad ya yi godiya ga gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa

Sannan ya bada tabbacin kudirin rundunar ‘yan sandan wajen ganin an yi maganin matsalar tsaro a jihar Katsina kuma ya bada tabbacin za a yi amfani da motocin kamar ka’ida ta nuna.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *