Gwamna Zulum Ya Bayyana Zaɓen Sanata Shettima Mataimakin Tinubu Mataki Mafi Cancanta Ga Nijeriya
Daga Muhammad Maitela
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana zavo Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakin takarar shugaban qasa a jam’iyyar APC wanda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi a matsayin hangen nesa kuma mataki mafi dacewa da cancanta.
Zulum ya bayyana hakan a wata sanarwar manema labaru wadda ya sanya wa hannu kuma aka raba wa yan jaridu, da yammacin ranar Lahadi a birnin Maiduguri.
“Yau na yi matuqar farin-ciki dangane da muhimmin labarin sanarwar da ta riskeni cewa shugabana abin koyi, inda xan takarar shugaban qasarmu a jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zavi Sanata Kashim Shettima matsayin mataimakinsa.
Wanda ko shakka babu wannan shi ne babban burin da nake dashi na ganin Sanata Kashim Shettima ya samu wannan dama wadda ya cancanta kuma ya dace, a matsayin xaya daga cikin shugabani masu kishin Nijeriya a zukatansu.”
“A wajena, kuma ina da tabbacin kaso mai yawa a cikin shugabanni da yan jam’iyyar APC, sun yi na’am da wannan hangen nesa wanda Tinubu ya yi na zavo Sanata Kashim Shettima a daidai wannan lokaci na buqatar hakan.”
“Zavar Shettima al’amari ne wanda ya shafeni a qashin kaina, tare da shugabaninmu haxi da baki xayan masu ruwa da tsaki da mambobin jam’iyyar APC, wanda nake da tabbacin cewa zamu tashi tsaye haiqan, muyi aiki tuquru, babu dare ba rana wajen yaqin neman zave domin samun gagarumar nasara a zaven 2023, in Sha Allah.”
“Bugu da qari, ko shakka babu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi dacen zaven shugaba nagari, ya zavi mutumin da ya san Nijeriya ciki da bayanta tare da qalubalen da take fuskanta. Wanda a cikin qabilun da suke jihohin Nijeriya 36 haxi da Abuja, babu wanda Sanata Kashim Shettima ba zai gaza yin gamsasshen bayani a kansa ba. Saboda yadda yake da masaniya kan yanayin mu’amalarsu ta rayuwa, al’adu, addini, tsarin tattalin arziki, da tsarin siyasarsu- a dukan wadannan jihohi 36 haxi da Abuja.”
“Shettima haqiqanin xan kishin qasa ne, wanda ya yi imani kan haxin kan qasa, tare da tabbatar da hakan a wurare daban-daban a rayuwarsa.”
“A hannu guda kuma, abu mafi muhimmancin dai shi ne, Tinubu ya yi zavawa wa Nijeriya mataimakin shugaban qasa mai zuwas, in sha Allah, wanda kuma hakan mataki ne na hangen nesa tare da amfani da ilimi kuma a cikin cancanta, kuma hakan zai havaka ci gaban tattalin arzikin Nijeriya, duniya ma sai ta shaidi hakan.”
“Ina da abubuwan faxa masu yawan gaske dangane da Sanata Kashim Shettima, amma na taskace su har sai lokacin yaqin neman zave.”
“A hannu guda kuma, zan yi amfani da wannan dama wajen bayyana jinjina da girmamawa ga shugaban jam’iyyar mu, shugaban qasa Muhammadu Buhari, bisa kyakkyawan shugabancin da ya gudanar a cikin waxannan shekaru tare da cikakken goyon bayan zaven Sanata Shettima ya marawa xan takarar shugaban qasa.”
“Har wala yau kuma muna yaba wa shugabanin majalisar zartaswa na qasa a jam’iyyar APC tare da mambobin kwamitin qwararru da dattawanmu na jam’iyyar haxi da ilahirin masu ruwa da tsaki a gudanar da jam’iyyar APC.”
“Muna yaba wa jajircewar baki xayan Gwamnonin APC a qarqashin jagorancin babban yayana, Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu.”
“Haka zalika da dukan shugabanin jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki a Arewa Maso Gabas bisa cikakken goyon bayan su, shugabanin jam’iyyar APC a jihar Borno da ximbin magoya baya, muna matuqar godiya.” Gwamna Zulum.
