Gwamna Raɗɗa Ya buƙaci Al’umma da su Sanya Hannu Wajen Gina Masallatai Da Makarantun a Katsina
Gwamna Raɗɗa Ya buƙaci Al’umma da su Sanya Hannu Wajen Gina Masallatai Da Makarantun a Katsina
Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na jihar Katsina ya bukaci masu hannu da shuni da su gina masallatai da makarantun Islamiyya wadanda zasu taimaka wajen tarbiyyartar da al’umma.
Ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake kaddamar da wani sabon masallacin Juma’a a karamar hukumar Sandamu, wanda wani jami’in “yan sanda, AIG Mustafa Bala Sandamu, ya gina.
Gwamna Raɗɗa ya ce gina masallatai da makarantun islamiyya zai taimaka matuka wajen koyar da ilimi da kyawawan halaye wanda zai sa al’umma ta inganta.
Ya umurci kwamitin masallacin da al’ummar garin Sandamu da su rika ba masallacin irin kulan da ta dace tare da yin amfani da shi a matsayin cibiyar koyo da inganta tarbiyya.
A nasa jawabin, mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, ya mika godiyarsa a madadin al’ummar Sandamu da masarautar Daura ga wanda gina masallacin.
Sarkin ya kuma kaddamar da limami da mataimakin limamin masallacin da sauran ‘yan kwamitin masallacin tare da horarsu da kula da masallacin da yin wa’azi da tarbiyya ga al’uma.
Tun da farko a cikin hudubarsa ta Juma’a, limamin masallacin, Sheikh Abdulhadiy Aliyu Daura, ya bayyana gina masallaci a matsayin daya daga cikin ayyukan ibada da ke da dumbin lada a wurin Allah Madaukakin Sarki.
Ya kuma bukaci al’ummar musulmi da su ci gaba da yi wa shugabannin kasar nan a kowane mataki addu’a domin samun nasara wajen inganta walwala da jin dadin ‘yan kasa.
Taron kaddamar da masallacin ya samu halartar manyan jami’ai da suka hada da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Bala Abu Musawa, da ‘yan majalisar zartarwa na jihar Katsina da hakimai a masarautar Daura.
