‘Funtua Unity Foundation’ Ga Hon. Sani Lawal: Kai Shugaba ne Mai Nagarta Abin Koyi
Shugaban kungiyar haɗin Kan Mutanen Funtua Kwamared Mannir Suleiman ya bayyana shugaban ƙaramar hukumar Funtua mai barin gado a matsayin wani haziki wanda za a rika koyi da shi
Kwamared Mannir Suleiman ya fadi haka ne a lokacin da shugabanin kungiyar haɗin Kan Mutanen Funtua ta kai ziyarar ban girma ga shugaban ƙaramar hukumar Funtua.
Kwamared Mannir ya cigaba da cewa Alhaji Sani Sani mutum da ya buɗe kofar sa a buɗe domin al’umma kuma ya nuna gaskiya a lokacin gudanar da shugabancin da a karamar hukumar Funtua wanda ta kamata a taya shi murna.
A cewar kwamared Mannir Suleiman sun kai wannan ziyara ne domin su taya shi murnar kammala wa’adin mulkin sa sannan su yi masa fatan alheri da rokon Allah ya kawo babban rabo.
Haka kuma shugaban kungiyar haɗin Kan Mutanen Funtua ya ƙara da cewa wannan ziyara da kungiyar takai kaiwa masu ruwa da tsaki tana yi ne domin kulla alaƙa ta yan uwantaka a karamar hukumar Funtua.
Kazalika kwamared Mannir ya yi ƙarin haske da cewa babban abinda wannan kungiyar ta sanya gaba shine tabbatar da samar da ingantaccen ilimi da kiwon lafiya da taimakon marasa karfi tare da neman dama ta ayyuka duk suna cikin manufofin wannan tafiya.
Sannan ya yi kira ga shugaban ƙaramar hukumar Funtua mai barin gado Hon. Sani Lawal da ya yi ƙoƙarin riƙe mutuncin sa da riƙon amana wanda zai zama abin koyi ga sauran shugabanni.
Da yake jawabi shugaban ƙaramar hukumar Funtua mai barin gado Hon sani Lawal ya nuna jin daɗin sa da wannan ziyara.
Sai dai kuma Hon. Sani Lawal ya karfafi shugabanni wannan tafiya da su tashi tsaye su zage damtse wajen tunkarar duk wani ƙalubale domin samar da kyakkyawar cigaba a yankin Funtua
Shugaban ƙaramar hukumar ya yi kira ga sauran kungiyoyi da su haɗa hannu da wannan tafiya domin cimma nasarar da ake buƙata
Hon. Sani Lawal ya alƙawarin bada tasa gudummawa wajen samar da cigaba ga wannan ƙungiya tare da tabbatar da yankin Funtua ya ƙara kai wani mataki
Shima da yake nasa ta’aliki l, ma’ajin kungiyar haɗin Kan Mutanen Funtua Alhaji Nura Sulaiman Yandaki ya bayyana Hon. Sani Lawal a matsayin amintaccen mutum kuma abin koyi
Alhaji Nura Sulaiman wanda ya yi dogon jawabi akan irin yadda wannan ƙungiya ke tafiyar da ayyukan ta ya ce ba su da alaƙa ta nesa ko ta kusa da sha’anin siyasa.
