September 17, 2026

EFCC Ta Yi Nasarar Kwato Biliyan 27 Da Dala Miliyan 19 Daga Binciken Da Take Yi Wa Tsofafin Gwamnoni Da Ministoci

0

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’anati wato EFCC ta ce ta yi nasarar Kwato kuɗaɗen da aka sace daga wasu tsaffin gwamnoni da ministocin Nijeriya.

Haka kuma EFCC ta ƙara da cewa yanzu haka ta yi nasarar dawo daga Kuɗaɗen da suka kai naira biliyan N27,184,357,524.52 and $19,084,419.33 daga kuɗaɗen da aka sace mabanbanta

Ta kuma cigaba da cewa nan bada jimawa ba, zata fitar da rahoto ga al’umma akan wannan aiki da take yi na dawo da kudaden da tsofaffin gwamnoni da ministoci da kuma jami’an gwamnati suka sace ta hanyar samun takardun koke akan su.

Kamar yadda majiyamu ta jaridar Punch ta ruwaito ta ce hukumar EFCC din ta ƙaddamar da wani sabon bincike game da badaƙalar wasu kuɗaɗai da ake zargin jami’an gwamnati a ma’aikatar wutar lantarki da kuma ma’aikatan Gona

Kakakin hukumar EFCC Dele Oyewale ya bayyana haka a jiya laraba a jihar Lagos lokacin da yake zantawa da manema labarai a madadin Muƙadashin shugaban hukumar EFCC Abdulkarim Chukkol

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *