DCP Abba Kyari, Dariye, Nyame Na Cikin Koshin lafiya Inji hukumomin gidan yari.
Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari da mutanensa da kuma tsohon gwamna Joshua Dariye na jihar Filato da takwaran sa na jihar Taraba suna cikin koshin lafiya kuma suna tsare, kamar yadda hukumar gidan yarin Najeriya ta tabbatar.
Hukumomin sun tabbatar da kashe jami’an hukumar tsaro ta farin kaya na Civil Defence, tare da wasu fursunoni hudu dake gidan yarin Kujen bayanda ‘yan bindiga suka kai hari a cibiyar gyaran hali a daren ranar Talata.
Yayinda jami’in hulda da jama’a na hukumar gidan yarin Umar Abubakar ya ke tabbatar da lamari, ya ce “Har yanzu suna da sauran muhimman mutane a hannunsu”.
Sai dai wasu mazauna wurin sun shaida wa jaridar The Nation cewa, sun ruga saboda hare-haren.
