Danfara: An gurfanar da wata mata gaban kotu a jihar Ogun bisa zarginta da buga rasiɗan POS na bogi.
An gurfanar da wata mata yar shekaru 27 masu Mutiat Ajoke a gaban kotun majestire dake Ota a jihar Ogun jiya Alhamis bisa zarginta da yin rasiɗan bogi na POS har guda 117.
Ƴan sanda dai sun tuhumi Mrs. Ajoke da laifuka da suka haɗa da aikata sata da kuma gurza takardun bogi.
Lauya mai shigar da ƙara E.O. Adaraloye ya faɗa ma kotu cewa, wadda ake ɗara ta aikata laifin ne tsakanin watan Janairun shekarar 2020 zuwa watan Janairun shekarar 2022 a unguwar Payee dake Ota.
Adaraloye ya ce wadda ake ƙarar ta na aiki ne da wani kamfanin mai suna Payee Ventures, inda ta hakan ne ta samu damar yin rub-da-ciki da naira miliyan 17.9 mallakin wani mai suna Vera Odjugo.
Ya ce laifukan sun saɓa ma sashe na 390(6) da kuma sashe na 467 na kundun manyan laifuka na dokokin jihar Ogun.
Saidai wadda ake tuhumar bata amsa laifukan ba.
Kuma alkalin kuton mai suna A.O. Adeyemi ta bada wadda ake ƙarar beli akan naira 500,000, tare da kawo masu tsaya mata guda 2.
Ta kuma ce dole su kasance ma’aikatan gwamnati kuma suna da shaidar biyan haraji ga gwamnatin jihar ta Ogun.
Daga ƙarshe ta kuma dage sauraren ƙarar zuwa ranar 17 ga watan Fabarairu.
