Dan Takarar Majalisar Dokokin Jihar Kano Na Jam’iyyar ADC A Karamar Hukumar Rogo Ya Fadi Dalilansa Na Fitowa Takara.
Babangida Sanusi Kano
Dan takarar majalisar dokokin jihar Kano na jam’iyyar ADC a karamar hukumar Rogo Haruna Yahaya Kadana ya bayyana irin matsalolin da suka sha gaban karamar hukumar Rogo da suka sa shi fitowa takara dan nemo hanyoyin kawo sauyi mai ma’ana ga al’ummar yankin.
Haruna Kadana wanda ya bayyana hakan yayin da yake ma jaridar Popular News Hausa karin haske kan kudurinsa, ya ce karamar hukumar Rogo nada rashin wasu ayukan more rayuwa a halin yanzu kuma idan ya samu nasara zai kawo chanji mai dorewa.
Kadana ya misalta jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyya mai san kawo sauyi ba tare da duba banbancin addini ko kabila ba. Ya basu damar dakko ta matsayin jam’iyya mafita ga yan karamar hukumar Rogo da jiha har da matakin kasa a zabe mai zuwa.
“Ina kallon wannan dama ce ta kara taimakon mata da matasa hadi da dalibai wajen taimakon rayuwarsu da samun ilimi idan mun samu nasara.” Inji shi.
Sannan ya yi nuni da cewa dan takarar kujerar gwamnan jihar kano Malam Ibrahim Khalil da yake jagora ga al’umma Kuma shugaba abin koyi, dan haka ko tanan jama’a zasu iya fahimtar lallai tafiya Yan takarar ADC babu wasa a tare da su.
Sannan ya ce lallai lokaci yayi da jama’a za su yi ma kan su hisabi irin na siyasa wajen zaben shugabanni don yima su ayukan da za su kawo cigaba a yau da kullum da rayuwar su, tare da morewa daga wanda suka zaba.
“Sannan yanzu haka shirin gidauniyar sa na ba mata da matasa jari, tare da ba dalibai taimako wajen ilimi da sauran al’umma.” Inji shi.
Daga karshe ya bayyana wasu garuruwa irinsu Zoza da Zarewa, Gwangwan da sauran mazabu na Rogo babu wani abu da zai nuna kazo karamar hukumar Rogo banda sakatariya, inda kadana ya bukaci kowa ya samu ya karbi katin zaben sa don samun damar kaɗa kuri’arsa wajen zaben gwanin su day zai kawo cigaba gare su.
