DA DUMI-DUMIN SU| Ƴan Bindiga Sun Sace Yan Kasuwa Sama Da 70 Masu Tafiya Zuwa Kano.
Akalla ƴan kasuwa 70 ne dake niyyar tafiya Kano aka yi garkuwa da su a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna a ranar Laraba.
An bayyana cewa ƴan bindiga da dama ne suka kai wa ƴan kasuwar hari da safe, inda suka dauke su da karfin tsiya zuwa cikin dazuzzuka.
Wani dan yankin mai suna Malam Umaru ya shaida wa manema labaru cewa ƴan kasuwar na tafiya ne a cikin ayarin motoci sama da 20 tare da rakiyar ƴan sanda.
A cewarsa, “ƴan bindigar sun kai hari ne a wata kwana da ke kusa da Udawa bayan Buruku, sun yi awon gaba da ƴan kasuwa akalla 70 daga yankin da wasu da dama daga kauyukan da ke makwabtaka da wajen.
Mazaunin yankin ya fada cewa da ya kira wayar wasu daga cikin ƴan kasuwar da suka bace, ƴan bindiga ne suka amsa, lamarin da ya tabbatar da cewa ƴan kasuwar na hannun su.
Ana cigaba da dakon martanin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna kan lamarin har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoton.
Haka kuma, har yanzu gwamnatin jihar ba ta ce uffan a kan sace ƴan kasuwar ba.
Idan dai ba a manta ba a ranar Talatar da ta gabata ne Gwamna Nasir El-Rufai ya je fadar gwamnatin tarayya inda ya tattauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan matsalar rashin tsaro a jihar inda gwamnan ya koka da yadda matsalar tsaro ke cigaba da ƙara munana a jihar ta Kaduna.
