Cin Zarafi: Gwamnati Ta Gurfanar Da Mutane 50 a Gaban Kuliya Manta Sabo A Katsina
Daga Sadiya Sani Sadiƙ
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa kimanin mutane hamsin ne ta gurfanar a gaban kotuna daban-daban akan zargin cin zarafin Ɗan Adam a Katsina.
Kwamishiniyar harkokin shari’a kuma Antoni janar ta jihar Katsina, Barista Fadila Dikko ce ta bayyana haka ga manema labarai a Katsina.
Barista Fadila Dikko ya ƙara da cewa waɗanda aka zarga laifuffukan cin zarafin dan Adam sun fito ne daga ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina
A cewar ta, idan ba a manta a shekarar 2024 gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya saka hannu akan sabuwar dokar akan cin zarafin dan Adam tare da alkawarin yin aiki da dokar ba sani ba sabo.
Haka kuma kwamishiniyar shari’ar ta nanata kudirin gwamantin jihar Katsina na hukunta duk wanda aka samu da laifin cin zarafin dan Adam doka zata rufe ido ta yi aiki a kan sa.
Shima da yake ƙarin haske baban sakataren a ma’aikatar Shari’a ta jihar Katsina Barista Muhammad Rabi’u Kumasi ya ja hankalin al’umma da su guji aikata laifin fyaɗe a cikin al’umma.
Yana mai cewa babu wanda zai so ayi wa wani na shi cin zarafi, ya ƙara da cewa dole al’umma ya kauracewa aibata iyayen da iftila’in fyaɗe ya afkawa yaran su domin gudun tsangwama a cikin jama’a.
Barista Muhammad Kumasi ya jaddada aniyar gwamantin jihar Katsina na bin kadi da bibiyar duk wani da ake zargi da laifin cin zarafin ‘ya ‘ya mata wanda ya ce dole shari’a ta yi aikin ta akan ko wanene.
