Ban Taɓa Ganin Shugaba Mara Tausayi Kamar Shugaba Buhari Ba, Tanko Yakasai
Tsohon hadimi ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, wato Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana cewar bai taɓa ganin shugaba mara tausayi kamar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba.
Yakasai ya bayyana haka ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, akan matsalar tsaro da ta addabi yanki Arewacin Najeriya wadda taƙi ci taƙi cinyewa.
Inda ya bayyana cewar:
“Har ga Allah, ba na jin dadin posting akan matsalar tsaro, har ga Allah ba ni da wata manufa ta tozarta gwamnati ko amfani da matsalar tsaro wajen nema suna ko siyasantar da maganar tsaro, har ga Allah ina rokon Allah Ya bawa shugabannin mu da jami’an tsaro nasarar shawo kan matsalar, amma duk wani uzuri da zan iya yiwa gwamnatin nan akan maganar tsaro na yi, amma abu yaki karewa.”
“Ni na san cewa irin yakin sunkurun da ‘yan bindiga da ‘yan fashin daji suke yi, abu ne mai wuyar shawo wa ta farat ta daya, amma gaskiya rashin ko in kula da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari take yi na halin da arewa take ciki shi yafi kona min rai.”
“Ban taba ganin shugaba mara tausayi ba kamar shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ce ko jaje baza kai wa mutane ba an kashe musu yan’uwa, ba sau daya ba ba sau biyu ba. Kuma kai ka roki mutane su zabe ka, kuma sharadi na farko da kundin tsarin mulki ya rataya maka shine kula da rayuka da dukiyoyin mutanen kasar nan, amma ko a jikin ka. Shin baka san jajantawar nan, da nuna damuwa yana rage radadin zafin rashin da mutane suka yi ba na kisan yan’uwan su? Shin baka san jajintawar da zaka musu za ta ba su kwarin gwiwa ba, akan cewa kana iya kokarin ka?”
“Duk shugabannin Najeriya ko na jiha ko na taraiya babu wanda yake da kima da mutunci da daraja a idanun mafi yawancin yan Najeriya kudu da arewa kamar Gwamnan Borno, Zulum. Saboda kowa ya yarda ya na da kishin al’umar sa, abinda ya shafe su ya shafe shi, kuma ya damu da halin da suke ciki, sannan ya na iya bakin kokarin sa ya ga cewa ya sauke nauyin da Allah Ya dora masa. Wannan shine shugabanci ingantacce. Amma da kai da Gwamnonin jihohin da matsalar tsaro tai tsamari, ba irin wannan halin ne da ku ba ga al’umar ku, kuma wannan abu ne da Allah sai ya tambaye ku gaba daya.”
“Mu nauyin da ya rataya a wuyan mu, mun sauke shi. Namu dama mu fada ne kuma mun fada, zamu ci gaba da adduah domin na tabbatar adduah bata faduwa kasa banza, In sha Allah, Allah zai karbi adduar mu Yai mana maganin matsalar nan. Ku kuma shugabanni kusan cewa Allah zai tuhume ku akan wannan nauyi da ya rataya akan ku. Dan haka ku ji tsoron Allah, Ku guji ranar da zaku tsaya a gaban sa domin hisabi, dan wannan rana ta na zuwa. Allah kai mana rahama da rahamar Ka, kai mana sauki da saukin Ka, Ya Allah Ka kawo mana karshen wannan masifa. Amin Ya Rahman.”
Salihu Tanko Yakasai (Dawisu)
Former S.A
Masoyin Kano da Arewa da Najeriya
