September 17, 2026

Ban Gamsu Da Yadda Aikin Gina Gidaje 250 Na ‘Renewed Hope’ Ke Tafiya A Katsina Ba -Darma.

FB_IMG_1780294483504

 

Ministan gidaje da raye birane Injiniya Muttaƙa Rabe Darma ya bayyana rashin gansuwa da yadda aikin gina gidaje 250 da gwamnatin Tinubu ke yi ƙarƙashin shirin ‘Renewed Hope’ a jihar Katsina.

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin wata ziyarar gani da ido akan yadda aikin ke tafiya a rukunin gidajen da kusa da jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina

Injiniya Muttaƙa Rabe Darma ya ce a rahotan da ya karanta a ofis ya nuna cewa an kammala waɗannan gidaje 250 saɓanin abinda ya gani da idon sa a lokacin wannan ziyara.

“An rubuta a rahoto cewa gidaje 250 ƙarƙashin shirin shugaban ƙasa na “Renewed Hope’ an kammala su a Katsina baƙi ɗaya, amma da na zo guda 130 ne kawai aka kammala kamar yadda kowa ke gani.” Inji shi

A cewar sa, ya bada umarnin a nemi ‘yan kwangilar domin jin dalilin su na kin kammala wannan aiki kamar yadda aka kulla yarjejeniyar da su tun farko kuma suka sanya hannu.

Injiniya Muttaƙa Darma ya yi barazanar ɗaukar mataki akan duk ɗan kwangilar da aka samu da saɓa alƙawarin ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Ya ƙara da cewa a yarjejeniyar da aka kulla da ‘yan kwangilar shi ne za su kammala wannan aiki a cikin wata shida, inda yanzu kimanin shekara ɗaya da rabi ke nan da bada wannan aiki, ba a kammala ba kuma babu wani bayani a rubuce daga wajen ‘yan kwangilar.

Ministan ya ce babu inda aka yi batun ƙara wa’adin kwangilar a yarjejeniyar da aka kulla tsakanin su da gwamnati kafin a ba su aiki, wanda ya ce babu wani dalili da ‘yan kwangilar za su ba shi na kin kammala aikin cikin lokaci.

Ya ce dangane da batun ɗaukar mataki kuwa zai ta’alaƙa ne da wanda bai kammala na shi aikin ba, amma wanda ya kammala ba za su dauki kowane irin mataki akan sa ba.

About The Author