September 18, 2026

Bamu Da Alaƙa Da Faifan Muryar Dake Cewa Sai An Biya Kudi Kanan Ayi Ma Mutane Rijistar Samun Tallafi — SOCU.

0

Ofishin kula da rijistar mutane masu ƙaramin karfi na jihar Katsina watau SOCU karkashin shirin samar da ingantacciyar rayuwa ga al’umma na kasa ya ce aikin rijistar karɓar bayanan gidajen mutane masu ƙaramin ƙarfi, a ƙananan hukumomi 20 na Jihar Katsina kyauta ne.

Bayanin hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na ofishin marwana Abubakar Darma ya fitar, Popular News Hausa.

Sanarwar ta ambato jami’in kula da shirin na jihar Katsina ya na gargadin al’umma dasu nisanta kansu daga masu damfara da suka fitar da wani faifai murya dake bayyana cewa, sai mutane sun biya kudi kafin ayi masu rijistar shiga cikin shirin.

Aliyu Isah Girka ya ce sashen bai da wata alaƙa da yan damfarar, tare da gargadin al’umma da su nisanta kansu daga dukkan wani aiki na zamba.

Aliyu Girka ya bayyana cewa ofishin na aiki ne da kananan hukumomin da sarakunan gargajiya da kuma shuwagabannin al’umma domin zabo wadanda suka cancanta su amfana da shi.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *