Awa 48 Da Bada Tallafi: Sunan Hon. Sani Aliyu Danlami Ne Mafi Ambato acikin Birnin Katsina
Awa 48 Da Bada Tallafi: Sunan Hon. Sani Aliyu Danlami Ne Mafi Ambato acikin Birnin Katsina
Rahotannin da suke yawo a tsakanin al’umma a cikin birnin Katsina na nuni da irin yadda rabon tallafin da Hon. Sani Aliyu Danlami ya yi matuƙar tasiri ga waɗanda abin ya shafa.
Dole ne irin wannan abin alheri ya ratsa zukatan jama’a, musamman idan kasan wanene Hon. Sani Aliyu Danlami Mai Raba Alheri, ga wadanda suke adawa da shi kuwa duk jikin su ya sanyi, domin daman an ce alheri mai hana mugun suna.

Babu shakka mai raba alheri ya raba kuma masu amsar alheri sun amsa, wannan ta sa a cikin kwana biyu babu wani zance mai ma’ana da ya wuce ta ya jina murna musamman waɗanda Allah ya tsaga da rabon a wannan tallafi.
Da yawa daga cikin waɗanda suka amfana da wannan tallafi an ce ba wanda yasan da wannan zancen, sai dai kira kawai suka ji cewa mai raba alheri ya yi kira, kuma sun amsa kira.

Tuberin mai shayi manyan majalisun hira, gidajen aure da wuraren sana’a sun kasance tamkar ana jiran sakamakon zaɓe, ma’ana dai babu abinda ake tattaunawa sai irin namijin kokarin da ɗan majalisa mai wakilta Katsina ta tsakiya ya yi na rabon kayan tallafi.
Abubuwan da ɗan majalisar ya raba sun haɗa da motoci guda 20 da Hijet guda 20 sai mashina 150 da kekunan ɗinki 150 da injinan fachi 150 da injinan Ban ruwa 150 da kuma kuɗi har Naira miliyan 60 lakadan.
Hakika wannan lamari ya zo ne a daidai lokacin da wasu ke alamta cewa Hon. Sani Aliyu Danlami ya ja baya a siyasa, ashe sabon shiri ya yi. Ko yanzu kwalliya ta biya kuɗin sabulu a Katsina ta tsakiya.

Jerin abubuwan da ɗan majalisar ya raba na daga cikin abubuwan ban mamakin da aka fi tattauna batun akan su, musamman ganin cewa ko shekara biyu bai cika ba akan wannan kujera, sai dai an yi hasashen cewa abinda ya yi kila sai nan gaba, wani ya ɗora daga inda ya tsaya.
Daga cikin abubuwan da aka raba a matsayin tallafi akwai motoci irin daban-daban ciki harda Hilux domin baiwa jami’an tsaro da kuma motoci na alfarma da Hijet domin masu sana’a.
Sannan akwai motoci irin na kece raini waɗanda sai wane da wane ga kuma mashina da aka rabawa matasa domin dogaro da kai musamman a wannan lokaci da sana’a ta yi wuya.
Mai Raba Alheri bai tsaya nan ba, sai da ya ƙara daga darajar mata inda suma ya gwangwaje su da kekunan ɗinki irin na zamani, wannan lamari ya yi wa Yan uwa da abokan arzikin duk wadanda suka samu wannan tallafi.
Baya ga haka, akwai tsabar kudi da aka raba a matsayin tallafi wanda suka fara daga Naira dubu ɗari biyar abinda ya yi sama, shima duk don a karfafa matasa su tsunduma cikin neman na kan su.
Yadda ake tattauna wannan batu a kafafen sadarwa na zamani kuwa, rahotannin sun nuna cewa batun na iya daukar dogon lokaci ana tattauna shi, ana cigaba da yi wa juna murna, ana Allah ya maimaita, wasu kuma na faɗin shikenan ya ƙara zama abin kwatance wajen ayyukan alheri.
Sai dai wasu bayanai sirri sun bayyana cewa Hon. Sani Aliyu Danlami yana wani shiri na ƙara daukaka darajar yan jarida wanda ya ce sune abokan nasarar shi, bayanan suka ce gaban kaɗan za a ga ta inda zai bulluwa yar jarida wajen daga darajar aikin su a idon duniya
