Asibitin ƙwararru Ta Nasarawa Zata Yi Bikin Rufe Gawarwaki Goma Da Ba a San Masu Su Ba
Daga Auwal Isah
Asibitin ƙwararru (Federal Medical Centre) da ke Keffi a jihar Nasarawa za ta binne wasu gawarwaki 10 da ba a san masu ba.
Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama’a na asibitin Muhammad Adamu ya fitar.
Kamar yadda ya bayyana, jami’an ƴan sanda ne dana hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa suka kai gawarwakin ajiya a asibitin tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020.
Muhammad Adamu ya kuma ce adadin watanni 6 ne kacal doka ta ba asibitin damar aje gawa kuma hakan ya wuce, saboda haka asibitin ta ba masu kula da sashen aje gawarwaki umarnin bada dama ga duk wanda ya zo ya na neman ɗan uwanshi ya shiga ya duba ko a dace.
Daga nan sai ya ce idan wannan sanarwa da aka fitar ranar 8 ga watan Fabarairu shekarar wannan shekarar ta 2022 ta cika mako 2 ba tare da masu gawarwakin sun zo amsar kayansu ba, to hukumar gudanarwar asibiti ba ta da wani zaɓi da ya wuce na bunne su.
