Arch Ahmad Musa Ɗangiwa: Halin Mutum Jarinsa
Daga Aliyu Abdullahi Gora II
Ahmed Musa Dangiwa, Shi ne dan Takarar Kujerar Gwamnan jihar Katsina Mafi Cancanta Bisa Bayyanannun Dalilai 10.
- Tun kafin ya shiga siyasa, ya kafa kamfanonin da su ka samar da guraben aiki ga daruruwan matasa.
- Ba a taba samun shi, ko kuma zargin shi da cin dukiyar al’umma ba.
- Tun su na ANPP, Dangiwa bai taba raba hanya da shugaba Buhari ba.
- A matsayin shi na shugaban Bankin Bada Lamunin Gidaje, Dangiwa ya tabbatar wa duniya cewa lallai shi mai kishin jihar Katsina ne.
- Bai taba canza ma wani fuska saboda bambancin ra’ayin siyasa ba.
- Har gobe babu mai iya nuna abokin gabar Ahmed Dangiwa.
- Mutum ne mai sauraren kowa ba tare da la’akari da matsayi ko girman mukami ba.
- Bai taba yi wa gwamnatin masari shisshigi ta kowace fuska ba.
- Ya na daga cikin mutanen da shugaba Buhari ya gamsu da gaskiya da rikon amanar su.
- Babu wanda ya taba shaidar shi da aikata wani aikin assha.
Wadannan su ne kadan daga cikin dalilan da su ka sa Ahmed Dangiwa ya bambanta da sauran ‘yan takara ta fuskar Nagarta.
