Anyi Bikin Ranar Mata Ya Duniya Amma Su ne Suka fi Kowa Shan Ukubar Rayuwa – Gamayyar Kungiyoyin Farar Hula A Katsina
Gamayyar Kungiyoyin Farar hula a jihar Katsina sun bayyana cewa a daidai lokacin da ake gudanar da bikin ranar mata ta duniya sai dai kuma mata ne suka fi kowa shan baƙar wahala a wannan duniya.
Shugaban gamayyar Kungiyoyin a jihar Katsina Malam Abdulrahaman Abdullahi Dutsinma ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma ya rabawa manema labarai a Katsina.
Sanarwar ta ce, a daidai lokacin wannan biki na mata, bayan ta su murna dole ta riƙa tunawa da irin abubuwan da suke samun mata a cikin al’umma mai kyau da marar kyau.
“An ƙara samun tsananin rayuwa a dalilin cire tallafin man fetur, sannan kullum sai an rasa rayukan al’umma sakamakon ayyukan ‘yan bindiga ga yawaitar fyaɗe ga ‘ya ‘ya mata da keta haddi su a jihar Katsina” inji sanarwar.
Kazalika kungiyoyin sun nuna takaicin su akan yadda matsalar tsaro ta rikewa tattalin arziki wuya a jihar Katsina tare da rasa rayuka saboda ayyukan ‘yan ta’ada.
A cewar sanarwar, duk da cewa harkar noma ita ce babbar hanyar kuɗaɗen shiga a jihar Katsina, ta ce abin takaici da baƙin ciki shi ne, ayyukan ‘yan bindiga sun raba jama’a da dama da gonakin su.
Ta ƙara da cewa hakan ya taimaka matuƙa gaya wajan haifar da talauci wanda a sanadiyar haka, matasa na tururuwa cikin ayyukan ‘yan ta’ada wanda daga ƙarshe mata da ƙananan yara ne ke cutuwa.
Sannan gamayyar Kungiyoyin Farar hula sun yi tsinkayen cewa tun shekarar 2023 da gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur rayuwa ta cigaba da zama baban kalubale, kayayyakin Abinci kullum sai ƙara kuɗi suke yi amma hanyar samun kuɗaɗen kuma tana raguwa so sai.
Haka kuma gamayyar Kungiyoyin Farar hula sun yaba da irin ƙoƙarin gwamnatin jihar Katsina wajen yaƙi da ‘yan bindiga domin samar da zaman lafiya.
Sai dai ta ce wannan yaƙi zai iya samun nasara ne idan al’umma sun bada haɗin kai da goyon bayan da ake buƙata domin kaiwa ga nasara.
“Abin baƙin ciki da takaice shi ne yau kimanin watanni 10 da cire tallafin man fetur amma babu wata mafita da gwamnatin tarayya ta bullo da ita domin samar da isashen man fetur kuma mai sauki ga al’umma.
Inda kungiyar ta nuna takaicin ta da cewa babu matatar Mai koda guda ɗaya a Nijeriya da take aikin tace mai domin samun sauki ga al’umma
