An Yi Addu’ar Neman Zaman Lafiya A Masallacin Masjudun Nur Filin Polo Katsina.
Sanannan Malamin addinin Musluncin nan Malam Iyal Gafai, Limamin masallacin Juma’a Na Masjudun Nur dake unguwar Filin Polo cikin Katsina Dr. Ibrahim Iyal Gafai da sauran hadiman masallacin da suka haɗa da Malam Kabir Sufi, Malam Murtala da kuma Malam Naziru suka yi addu’ar domin ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiha dama kasa baki ɗaya jim kaɗan da kammala sallar Juma’a a masallacin.
Sannan sun bayani mai tsawo akan falalar taimakawa addinin Allah, inda suka yi kira ga masu hannu da shuni su riƙa gina addinin Allah da abinda Allah ya hore masu.
Malaman dai sun gode ma Allah SWA bisa samun masallacin, tare da roƙon ya kaima wanda aka gina masallacin don shi ladar.
Idan dai ba a manta ba, Dahiru Mangal ne ya gina masallacin da Islamiyya da niyar Allah ya kaima ɗan shi Muhammad Nura da Allah ya yima rasuwa sanadiyyar haɗari da matsin ladar.
Kuma masallacin da Islamiyya da ɗunbin mutane ke cin gajiyar su, masallacin shekarar shi ɗaya kenan da ginawa.
