September 17, 2026

An shirya taron horaswa na kwana guda domin ƙarfafa ƙwarewar masu taimaka wa gwamnatin Jihar Katsina

WhatsApp-Image-2026-05-09-at-17.10.51

 

Taron dai na da nufin samar da wani ilmi a harkar yaɗa labarai da hulɗa da kafafen sada zumunta a domin amfani da ƙarfin kafafen sada zumunta da kirkirariyar fasahar zamani (AI)

 

Haka kuma ana bukatar mahalarata taron su samu ƙwarewa wajen sadarwa mai inganci da aiwatar da manufofin gwamnati yadda ya kamata.

Da yake jawabi a wajen taron darakta janar na yaɗa labaran gwamnatin jihar Katsina, Malam Maiwada Dammallam ya ce an shirya taron ne domin haɗa jami’an yaɗa labarai da mataimaka daga ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyi daban-daban na gwamnatin jihar Katsina

 

Haka kuma Dan-Mallam ya buƙaci mahalarta taron da su mai da hankali sosai yayin zaman horaswar domin su samu cikakkiyar fa’ida da za ta ƙara musu ƙwarewa tare da inganta dabarun sadarwar gwamnati.

Ya ƙara da cewa tasirin sadarwar zamani da kirkirariyar fasahar zamani na ƙaruwa sosai, wanda hakan ya sanya wajibi ga masu kula da harkar yaɗa labarai su dace da sabbin hanyoyin yaɗa bayanai na duniya.

 

“Muna rayuwa ne a duniyar sadarwa. A yanzu akwai wata muhimmiyar hanyar sadarwa da ake amfani da ita a duniya baki ɗaya, wato kirkirariyar fasahar zamani (AI), musamman wajen sadarwa ta zamani,” in ji shi.

 

A cewar sa, kafafen sada zumunta yanzu sun fi sauri, sauƙi da dacewa wajen isar da saƙo idan aka kwatanta da tsofaffin hanyoyin sadarwa.

 

“Saboda haka, ina roƙon ku da ku mai da hankali sosai a wannan taro, domin na yi imanin za ku zama ƙwararru masu cikakken sani bayan wannan horaswa,” in ji Dam-Mallam.

 

Shima da yake nasa jawabin shugaban kamfanin Optimal image Media limited kuma daya daga cikin waɗanda suka bada horo, Alhaji Shu’aibu Mungadi, ya jaddada cewa kirkirariyar fasahar zamani ta zama muhimmiyar hanyar sadarwa da ake amfani da ita a duniya wajen hulɗa da jama’a da yaɗa bayanai.

 

“Kafafen sada zumunta sun tabbatar da cewa sun fi sauri, sauƙi da dacewa fiye da hanyoyin sadarwa na gargajiya wajen kai saƙo ga jama’a masu yawa da kuma tasiri wajen gina fahimtar jama’a.” inji shi

 

Ya bayyana cewa an tsara taron ne domin bai wa mahalarta ƙwarewa ta aikace da dabarun zamani wajen amfani da kafafen sada zumunta da fasahar AI a harkar sadarwa da aiwatar da manufofin gwamnati.

 

“Ina fatan cewa a ƙarshen wannan horaswa, tare da irin ƙwararrun malamai da aka tanada, har waɗanda ba su da cikakken sani a baya za su samu ilimi da ƙwarewar da za ta amfani aikinsu,” in ji Mungadi

 

Ya kuma buƙaci mahalarta taron da su riƙa tattaunawa da masu horaswa ta hanyar yin tambayoyi da neman ƙarin bayani har sai sun fahimci yadda ake amfani da kafafen sada zumunta da kayan aiki.

About The Author