An Shirya Ma Majalisar Jihar Katsina Ta 8 Taron Bada Horo.
Majalisar dokokin jihar Katsina ta shirya bada horon shiga ofis na kwana 4 ga membobin majalisa ta 8 da ya gudana Otel ɗin Port Golf da ke Kano.
Da yake buɗe taron, kakakin majalisar dokokin Nasiru Yahaya Daura ya bayyana sa ran cewa, bada horon zai ba mahalarta horon damar sanin ilimin dangantakar da ke tsakanin bangaren zartarwa dana majalisar dokokin.
Kakakin majalisar dokokin ya bayyana cewa, a karshen taron za a haska ma yan majalisar dokokin yadda zasu gudanar da ayyukansu.
A lokacin bada horon na kwana 4, Dr. Muhammad Mukhtar na jami’ar Maryam Abacha da American University da ke Kano da Maradi ya gabatar da wata takarda akan “Yadda Za A Gudanar Da kasafin kudin a ɓangarorin gwamnati.
Shima tsohon akawun majalissar dokokin Abubakar Ibrahim Dankanda ya gabatar da wata takarda akan tsare tsaren majalisar dokokin.
