An sanya Naira 31,500 a matsayin mafi ƙarancin kuɗin Sadaki ga al’ummar Musulmi.
An sanya Naira 31,500 a matsayin mafi ƙarancin kuɗin sadaki ga al’ummar Musulmi
Hakan na zuwa ne bayan zaman majalisar da ya gudana a sakatariyar ta da ke kan hanyar Kofar Sauri a Katsina.
Shugaban kwamitin duba batun kuɗin sadakin Farfesa Abdul’aziz Mashi ya ce a sanya wannan adadin kuɗin a matsayin mafi ƙarancin kuɗin sadaki ne biyo bayan yin la’akari da matsin tattalin arziki da ake fama da shi a halin yanzu.
Farfesa Mashi ya ce kwamitin ya samo hujja daga cikin Alkur’ani mai girma da Hadisin Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi.
Farfesa Mashi ya bayyana cewa kwamitin ya sanya Naira 52,500 a matsayin kuɗin Zakka ga mutanen da Allah ya mallaka mashi Naira miliyan 2.1.
A halin da ake ciki kuma, shugaban majalisar malamai na jihar Katsina Sheikh Nazir Kofar Baru Daura ya yi kira ga Malamai su yi wa’azi akan buƙatar yin haƙuri tsakanin al’ummar Muslimi a cikin watan azumi.
Shugaban wanda ke magana a lokacin taron majalisar, ya kuma gargaɗi al’ummar musulmi akan ayyukan da suka saɓa doka da zasu iya kawo tarnaki ga zaman lafiya masamman ma a cikin watan azumi.
Shina da yake magana, sakataren majalisar Sheikh Abubakar Adoro ya buƙaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya duba batun yiyuwar maido da tallafin man fetur.
