November 18, 2026

An Kashe Wani Lokacin Da Ake Gwajin Bindiga Kirar Gida A Jihar Delta.

0

Wani matashi dan shekara 26 Mr. Ogaga Kome ya harbe wani yaro dan shekara 11 da haihuwa mai suna Hossanna Merritt har lahira a lokacin da yake gwada wata bindiga kirar gida a garin Ozoro da ke karamar hukumar Isoko ta Arewa a jihar Delta, inji majiyar Popular News Hausa ta Vanguard.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Mr. Bright Edafe, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce wanda ake zargin da ya gudu bayan faruwar lamarin, an kama shi kuma a halin yanzu yana hannun ‘yan sanda.

Sanarwar ta kara da cewa, DPO na ofishin ‘yan sanda da ke Ozoro a ranar 22/8/2022, ya samu rahoton cewa “ ana zargin wani mai suna Ogaga Kome dan shekaru 26 da haihuwa ya harbe Hossanna Merritt ɗan shekaru 11 da haihuwa da ke Ozoro har lahira, tare da gudu bayan faruwar lamarin.

“Rundunar ta sanar da jama’a game da lamarin tare da neman bayanan da za su taimaka wajen kama wanda ake zargin.

“Saboda haka, a ranar 30/8/2022 da misalin karfe 01:05 na rana wani mutum mai kishin kasa wanda kuma dan uwan wanda ake zargin ne ya kawo shi ofishin yan sanda.

“Wanda ake zargin yana tsare hannun yan sanda, kuma ana ci gaba da bincike.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Delta, CP Ari Muhammed ya yaba wa kokarin al’ummar jihar wajen taimaka masu a yaki miyagun laifuka.”

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *