An Kafa Dokar Ta Ɓaci A Ƙaramar hukumar Ussa Ta Jihar Taraba
Shugaban karamar hukumar Ussa dake jihar Taraba Rimamsikwe Hassan ya kakaba dokar ta baci a yankin karamar hukumar
Matakin a cewarsa ya zama wajibi domin kawo karshen tashin hankalin dake cigaba da bazuwa tsakanin al’ummomin yankin musamamma ganin yadda ya ta’azzara a jiya jumma’a,daya haifar da asarar dukiyoyi masu tarin yawa.
Shugaban karamar hukumar yace mutane sun dauki doka a hannu ta hanyar afkawa junansu daga bisani yayi Karin haske kan dokar day ace tsakanin karfe 7 na maraice zuwa karfe 6 na safiya za tayi aiki.
