An Gano Gawarwaki 15, An Kona Gidaje 78 A Jihar Plateau – MACBAN
Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Najeriya (MACBAN) a jiya ta ce an kashe mutane 15 bayan wani farmaki da ake zargin an kai musu a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.
Kungiyar ta kuma ce an kona gidajen ƴaƴanta 78, yayin da sama da shanu 2,000 suka bace bayan kai harin, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Dailytrust ta bayyana.
Nuru Abdullahi, shugaban kungiyar na jihar ne ya bayyana hakan ga manema labarai jiya, a Jos, babban birnin jihar.
Jaridar Dailytrust ta ruwaito a ranar Asabar din da ta gabata yadda kungiyar ta zargi jami’an tsaron jihar na ‘Operation Rainbow’ da kai wa yankinsu hari tare da kona masu yanki, zargin da kuma rundunar ta musanta.
Ya ce, “Akan harin da aka kai wa Fulani a kauyukan Mangu, mun gano gawarwaki 15 da aka kashe a ranar Juma’a. Kimanin gidaje 78 ne aka kone. Shanu da adadinsu ya kai 2,000 har yanzu ba a gansu ba. Wannan abin takaicin na ci gaba da yaɗuwa har zuwa sauran kananan hukumomin jihar domin tarwatsa Fulani gaba daya a jihar.”
Abdullahi ya kuma yi zargin wani shiri na kai wa al’ummarsu hari da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne.
“Akwai rahoton sirri da ke nuna cewa akwai ‘yan bindiga da aka dauka aka kawo su yaki Fulani daga jihar Filato da sunan rikici. Don haka a halin yanzu muna kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kawo karshen abin da ke faruwa a karamar hukumar Mangu.
“Ya kamata su dauki matakin gaggawa kafin al’amura su wuce gona da iri. Muna rokon gwamnatin tarayya da ta dauki matakin da ya dace. Ba za mu ci gaba da kallon yadda mutane ke kashe mu da lalata mana dukiyoyi ba,” Abdullahi ya kara da cewa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, da na runduna ta uku ta sojojin Nijeriya, Rukuba Barrack, Laftanar Kanar Ishaku Sabastine Takwa, har yanzu ba su amsa kira da sakon da wakilin jaridar ya yi masa kan lamarin ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
Jaridar Dailytrust ta ruwaito cewa an samu rikici a kauyukan karamar hukumar Mangu inda aka tabbatar da mutuwar mutane sama da 200 da suka hada da mata da kananan yara a watannin baya.
A halin da ake ciki gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a karamar hukumar Mangu domin maido da doka da oda da kuma dakile asarar rayuka da dukiyoyi.
Daraktan yada labarai da hulda da jama’a, Gyang Bere, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce gwamnan ya sanya dokar ta-bacin ne bayan tattaunawa da kwamitin tsaro na jihar.
Gwamnan ya bada tabbacin cewa gwamnatin sa na aiki ba dare ba rana domin dawo da zaman lafiya da tsaro a jihar.
