September 18, 2026

An Fara Gudanar Da Ƙididigar Gidaje A jihar Kano

0

Daga Babangida Sunusi, Kano

Hukumar kidaya ta kasa reshen jihar kano tafara gudanar da kidaya ta trial census watau kidayar gidaje da a wasu Kananan hukumomi daga shiyyoyi ukku dake jihar kano.

Idan dai ana biye damu za’a iya tunawa cewa a makon daya gabane hukumar kidaya ta kasa tabada umarnin fara gudanar da wannan aikin na kidaya a fadin kasar na aka dauki tsawon lokaci ba gudanar ba.

Kamar yadda hukumar ta bada umarnin shelantawa kwanan baya cewa kowace jaha za’a gudanar da wannan aikin kidaya ta tun daga matakin gidaje yazuwa kan al’ummar Kananan hukumomi da hukumar tabada umarnin fara gudanar da aiki akowace shiyya Kuma kowace jaha.

Itama jahar kano tabi sauran takwarorinta na katsina,jigawa sokoto,inda ta fidda Kananan hukumomin Bichi,Kunchi da Danbatta daga shiyyar kudu.

Sai Kano ta arewa daya hada da Kibiya,Bunkure da karamar hukumar Rano, yayin da Kuma Kano ta tsakiya aka dauki Kananan hukumominMinjibir, Warawa da Garun Malam,kamar yadda takardar jaddawalin hukumar kidayar ta fitar.

Daga karshe kuma ajawabin mai girma kwamishinan kidaya ta jahar kano Alh Dr Sama’ila Lawal da daraktan hukumar kididdiga na jahar sun bukaci jama’ar da za’a gudanar da wannan aikin kidaya dasu ba ma’aikatan kidayar goyon baya tare da basu duk bayanan dasuka bukata daga garesu dan samun nasarar wannan aiki kafin zuwan kidayar bai daya ta shekarar 2023

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *