September 16, 2026

Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 9, Gidaje 6,417 Sun Lalace A Kano

0

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA) ta tabbatar da rushewar gidaje 6,417 da kadarori da kudinsu ya kai Naira miliyan 541.6 da ambaliyar ruwa da iska ta lalata a kananan hukumomi 10 daga watan Afrilu zuwa yau.

Sale Jili, babban sakataren hukumar SEMA ne ya tabbatar da hakan yau a Kano.

“Mutane tara ne suka mutu, gidaje 6,417 sun lalace, mutane tara suka jikkata, sannan anyi asarar dukiyoyin da kudinsu ya kai Naira miliyan 541.6 sakamakon ambaliyar ruwa da iska a jihar,” Mista Jili ya ce.

Ambaliyar ta shafi kananan hukumomin Doguwa, Kibiya, Kiru, Rano, Danbatta, Tsanyawa, Gwale, Ajingi, Dawakin Kudu da Albasu.

“Mun ziyarci Rano, Danbatta, Ajingi da Gwale domin raba kayan agaji ga wadanda abin ya shafa a matsayin matakan rage musu radadi,” inji shi.

Kayayyakin da aka raba wa wadanda abin ya shafa sun hada da kayan abinci, buhunan siminti, kwanikan rufi, tabarmi, barguna, matashin kai da man girki, da sauransu, in ji jami’in.

Shugaban na SEMA ya kuma bayyana cewa hukumar ta tura jami’ai zuwa dukkan kananan hukumomi 10 da abin ya shafa domin gudanar da tantancewa, domin ta samu damar samar da cikakkun bayanai da kuma taimakawa wadanda abin ya shafa.

Mista Jili ya yi kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani bala’i ga shugaban gundumarsu, ya kuma gargadi mazauna yankin da su daina zubar da shara a magudanan ruwa tare da share magudanun ruwa domin gujewa ambaliya.

Jami’in hukumar agajin gaggawar ya kara da cewa “Mazauna a kusa da wuraren da ake fama da ambaliyar ruwa su tashi su kare rayukansu da dukiyoyinsu.”

(NAN)

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *