AL’UMMA SUN NUNA RASHIN AMINCEWARSU GAME DA ƘUDIRIN DOKA WADDA ZA TA BA CIBIYAR NARICT DAMAR TA HAƊIYE AYYUKAN CIBIYAR NILEST TA ZARIYA
A tsarin mulkin dimokuraɗiyya irin wanda ake gudanarwa a Nijeriya, ɓangarori uku ne turakun da suke tafiyar da gwamnati, wato ɓangaren samar da doka da ɓangaren zartarwa da kuma ɓangaren shari’a.
Bangaren samar da dokokin ƙasa wanda yake alhakin majalisar wakilai ne da kuma majalisar dattijai, yana ba da gagarumar gudummawa wajen shimfiɗa dokokin da idan suka tsallake karatu daga majalisun kuma shugaban ƙasa ya sanya masu hannu, to suna sauya wasu al’amuran ko su tsirar da sababbin lamuran da suka shafi rayuwar yau da kullum ta al’umma.
A bisa irin wannan godabe ne a daidai wannan yanayi da ake ciki aka tsinci kai da batun ƙudirin doka mai lamba HB.2065, idan an sa mata hannu, za ta juya akalar ayyuka da ma’aikata da kadarorin Cibiyar Bincike kan Kimiyyar Fata ta Nigeria(NILEST) zuwa ga Cibiyar Bincike kan Fasahar Sinadarai ta Ƙasa(NARICT).
Ita Cibiyar Bincike kan Kimiyyar Fata ta Nijeriya(NILEST) ita kaɗai ce take samar da kwasa-kwasai na horarwa da bincike kan fatu da dangogin fasahohin da ake iya sarrafa fatu da dangoginsu. Ita kuwa Cibiyar Bincike kan Fasahar Sinadarai ta Ƙasa(NARICT) ayyukanta sun jiɓanci bincike ne kan sinadarai.
Hukumar Abinci da Ayyukan Gona ta Majalisar Ɗinkin Duniya ita ce ta kafa NILEST a matsayin Cibiyar Horarwa da Gwaje-gwajen Fatu da Ƙiraga a Samaru-Zariya tun a shekarar 1964.
A shekakar 1973 aka sauya mata suna zuwa Cibiyar Binciken Fatu ta Nijeriya(LERIN), kuma a 1978 ta koma ƙarƙashin Cibiyar Binciken Ayyukan Noma ta Nijeriya(ARCN), wadda a yau ita ce Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha da Ƙirƙira ta Tarayya (FMSTI).
Kafin shekarar 1991, NILEST tana ayyukan horarwa ne da bincike da samar da fatu da fasahohi madangantan su. A shekarar 1987 ne aka yi joni da fasahar sinadarai; hakan ya haifar da sauya sunan zuwa Cibiyar Bincike kan Fasahar Sinadarai ta Ƙasa(NARICT) a matsayin ɓangaren bincike da kuma Kwalejin Fasahar Fatu ta Tarayya(FCLT) a matsayin ɓangaren horarwa.
A shekarar 1992 ne aka sauya wa ɓangaren horarwar suna, wato daga Kwalejin Fasahar Fatu ta Tarayya zuwa Kwalejin Fasahar Fatu da Sinadarai ta Tarayya, kuma ta ci gashin kanta daga NARICT.
Haka kuma, a shekarar 2009 duk wasu ayyuka na bincike a kan fasahohin fata waɗanda NARICT ta cigaba da yi an mayar da su zuwa NILEST.
Bugu da ƙari, a ranar 1 ga watan Afrilun 2011 ne aka yi wa cibiyar gyaran fuska aka sauya mata suna daga Kwalejin Fasahar Fatu da Sinadarai ta Tarayya (CHETECH) zuwa Cibiyar Bincike kan Kimiyyar Fata ta Nigeria(NILEST). Wannan ya tabbatar da cewa, ita fa NARICT babu abin da ya shafe ta da bincike da horarwa a kan fasahar sarrafa fata, tun da aka riga aka ɗauke mata wannan nauyin a shekarar 2009.
Domin kuwa idan har za a bibiyi dokar da ta samar da cibiyoyin bincike kan ayyukan noma ta shekarar 1973 mai lamba 35, wadda ta samar da Cibiyar Binciken Fatu ta Nijeriya(LERIN), to fa NILEST ita ce za ta bugi ƙirji a kan wannan.
Saboda haka, idan har wannan sabuwar doka ta NARICT ta 2022 ta tsallake, tare da ƙare-ƙaren da aka yi a sashe na 5(1-6), kuma shugaban ƙasa ya sanya mata hannu a hakan, to tabbas za ta haifar da sa-toka-sa-katsi tsakanin cibiyoyin guda biyu, wato NARICT da NILEST.
Wani abin lura kuma shi ne, a watan Yuli na shekarar 2021 Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Dokar Kayayyakin Fata ta Ƙasa wadda wadda aka amince da ita tun a 2018. Kuma NILEST ita ce ta kasance unguwarzoma ta jagoranci da tabbatar da aiwatar da dokar domin jaddada irin damammakin da za a iya samu a ɓangaren, wajen cigaban tattakin arziƙin ƙasa.
Idan aka yi la’akari da yadda a gwammnatin dimokuraɗiyya ake ƙoƙarin jin ta-bakin al’umma kafin ƙaddamar da kowane ƙudiri ya zama doka, to babu shakka idan aka ce za a yi wannan haɗaka, za a yi abin nan da Hausawa ke cewa baya ba zani, domin kamar an kashe maciji ne ba a sare kansa ba.
Tutuɓe daɗin gushi, idan har aka aiwatar da wannan haɗaka, to fa abin ba zai haifar wa al’umma da ƙasa baki-ɗaya ɗa mai ido ba, domin kuwa dole ne wasu daga cikin ɓangarorin ayyukan da wata cibiyar cikin biyun suke gudanarwa su durƙushe.
Hakan zai iya haifar da rasa aikin yi tsakanin wasu ma’aikatan manya da ƙanana. Rashin aikin yi kuwa yana haifar da matsin tattalin arziƙi, wanda kuma shi ke haifar da ta’azzarar matsalar tsaro cikin al’umma.
Daɗin daɗawa, babu yadda za a ce an yi wannan gamayya kuma lamurra su bunƙasa, domin kuwa akwai yiwuwar kowane ɓangare sai an sake sabon lale. Sannan kuma idan aka duba abin da idon basira, za a ga cewa yin hakan ba shi ne abu muhimmi da al’umma take buƙata ba.
Domin kuwa duk wani ƙudirin doka da za gabatar, kamata ya yi a gabatar da ita ne domin cigaban al’umma da ma ƙasa baki-ɗaya. Ko ba komai, a kauce wa baya-ba-zani ko barin baya da ƙura !
