September 17, 2026

Aiki Bakon Raggo: Hon. Sani Aliyu Ɗanlami Ya Gwangwaje ‘Yan Kwamiti Da Sabbin Mashina

0

Daga El-Zaharadeen Umar

Hon. Sani Aliyu Ɗanlami Kwamshiinan jin daɗi da walwala da wassani na jihar Katsina ya gwamgwaje ‘yan sintiri masu kula da kwamitin unguwanni da sabbin Mashina domin samun sukunin yin aiki yadda ya da ce.

Al’ummomin da suka samu wannan tallafi sun hada da ‘yan kwamiti na unguwar ɗan Bedi da na kofar kwaya cikin birnin Katsina

Wannan gudunmawa na a matsayin wani tallafi ne daga Hon. Sani Aliyu Ɗanlami da ake yi wa kirari da mai raba alheri.

Tuni dai wadannan ‘yan kwamiti suka karbi wadannan Mashina domin fara gudanar da aikin su cikin nasara.

Mashinan dai kirar Boxer ne kuma sabbin fil da za a yi cewa jama’a su sa ido za su ga yadda aiki zan kankama daga wajan ‘yan kwamitin Sintiri da kofar kwaya da kuma ɗan Bedi cikin kwaryar Katsina

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *