A Yanzu an Samu Sauyi a Masana’antar Kannywood Ali Rabi’u Ali Daddy
DaGA Mukhtar Yakubu
Jarumi furodusa kuma Darakta a masana’antar Kannywood, Ali Rabi’u Ali Daddy, ya bayyana irin ci gaban da masana’antar Kannywood ta samu a matsayin wani gagarumin sauyi ta bangare ci gaban zamani.
Ali Rabi’u Ali Daddy ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar da muka yi da shi a matsayin sa na tsohon jarumi da ya shefe shekaru a cikin harkar fim.
Da farko dai ya fara da gabatar mana da kan sa kamar yadda muka yi masa tambayar sa wasu sun san shi wasu ba su san shi ba wasu kuma sun san shi, amma tsawon lokaci sun manta da shi, sai ya fara da cewa.

“To ni dai jarumi ne a masana’antar Kannywood sama da shekaru ashirin, don na faro tun daga matsayin mai daukar hoto na fara aktin, kuma a shekarar 1999 na fara shirya finafinai nawa na kaina, tare da aikin Daraktin, kuma har zuwa yanzu ana cikin harkar, kuma mafi yawan finafinai na ni nake rubutun labarin da kaina. To da haka aka taho, har Allah ya sa nima na fara samar da Jarumai na suka tsaya da kafar su a matsayin Jarumai.
Amma dai idan muka tafiyar da aka yi na tsawon lokaci za mu ga akwai ‘yan bambanci da aka samu ta ingancin labari, don a baya akwai labari mai ma’ana da tsari, yanzu kuma an samu tsari na ingancin kayan aiki ne.

Haka a bangaren Kasuwancin fim za ka ga a baya akwai hanyoyi da dama na samun Kasuwancin amma a yanzu hanya daya ce, ita ce ta Soshiyal Midiya, to amma dai da haka ake murzawa Allah yana bayar da abin da za a samu.
Samun kuɗi, a baya kowa ya san ana samu kuma akwai albarka. Kuɗin da ka samu ko da ba su da yawa za ka yi abubuwa na rufin asiri. Amma a yanzu magana ta gaskiya. A yanzu an fi samun kuɗi a fim fiye da lokacin baya.
Saboda ita kasuwar a baya idan ka yi kayan sai ka kaiwa wasu sun juya kudin sannan su ba ka. Yanzu kuma an samu damar da kan ka za ka nemi kudin ka a inda kake . To wannan za mu ga wani ci gaba ne da muka samu a wannan lokacin wanda za ka iya amfana da abin ka Kai tsaye .
Kuma idan Allah ya sa Mutum ya yi abin sa mai inganci aka yi nasara ana samun alheri sosai. Don haka ya kamata masu gudanar da harkar fim su rinka duba da yanayi da kuma lokatan da suke yin fim domin cin gajiyar harkar ta su.
Domin kamar yadda hanyar samun kudi ta baya da kuma ta yanzu ta bambanta, haka abubuwan za su ci gaba da tafiya, domin zamani yana tafiya ne, mu sai mu san yadda za mu tafiyar da Kasuwancin mu a duk yadda lokaci ya juya, ta haka ne za mu ci moriyar sana’ar mu kamar yadda kowacce sana’a take.”
