Gurɓataccen Man Fetur: Ƙungiyar ƴan Jarida Ta Buƙaci gwamnatin Tarayya Ta Biya ƴan Najeriya Kuɗin Diyya.
Daga Auwal Isah
Ƙungiyar ƴan jarida ta Najeriya (NUJ) ta buƙaci gwamnatin tarayya ta biya mutanen da gurɓataccen man fetur ɗin da aka shigo da shi cikin ƙasar ya lalata ma ababen hawa kuɗin diyya.
A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Mr. Chris Isiguzo ya fitar, ta yi nuni da cewa duk da an kwashe tsawon shekaru 4 ba tare da fuskantar matsalar yankewar man ba, amma a ƴan kwanakin nan ana fama da matsalar shi.
Kamar yadda shugaban ƙungiyar ya bayyana, hakan ya faru ne sakamakon shigowa cikin ƙasar nan da man fetur mai ɗauke da wasu sinadarai da suka wuce kima, saboda haka ya kamata masu hannu a ciki su ɗauki nauyin wannan asarar.
