YA KAMATA GWAMNATIN NAJERIYA TA KARAMA SHI
DAGA Datti Assalafiy
Marigayi DSP Abdullahi AbdulKadir Rano DPO na garin Jibia a jihar Katsina yayi mutuwa irin na jarumai wadanda suke sadaukar da rayukansu a fagen yaki
Da yaji labarin ‘yan ta’adda na zuwa, ba gudu yayi ba, bai buya ba, kayan yaki ya dauka ya fita shi da yaransa ya jagorancesu domin ya kalubalanci barayin, ya shiryawa shahada domin ya kubutar da rayuwarsu wasu
Matashin ‘dan sanda ne mai jini a jika, bai wuce shekaru 35 ba, yaro ne yana cikin ganiyar jin dadinsa da iyalansa, amma ya hakura da wannan rayuwar ya sadaukar da ita wa Gwamnatin Nigeria
Da wannan muke cewa ya kamata Gwamnatin Maigirma Shugaban kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya ta karrama DSP A.A Rano da lambar yabo na girmamawa tare da karin girma domin iyalansa su amfana a taimakesu, domin ya cancanci a masa hakan
Muna rokon Allah Ya karbi shahadarsa, Allah Ya kula masa da iyalansa
