Karya Ne Ba a Kashe Mutune 17 A Malumfashi Ta Jihar Katsina Ba – Rundunar ‘Yan Sanda
Rundunar Yan sanda a Jihar Katsina ta musanta rahoton kai hari da halaka mutane 17 a kauyen karfi dake karamar hukumar Malumfashi.
A tabakin kakakin rundunar ta Yan sanda a Jihar Katsina SP Isa Gambo yace labarin na kanzon kurege ne kawai.
SP Gambo yace sun tuntubi Jami’in dake kula da rundunar ta Yan sanda a Malumfashi akan lamarin inda ya tabbatar masu da babu makamancin wannan hari a kauyen da kuma halaka mutane 17.
Kamar yadda kakakin rundunar yace al’umma su guji yada labarai wadanda basu da sahihanci gudun hargitsa zaman lafiyar al’umma.
