Sabon Yunkurim Hon. Isah Kankara Na Bunƙasa Al’adu Da Wayar Da Kan Jama’a
Daga Hassan Male
A wani muhimmin yunkuri na cika manufofin Gwamnatin Jihar Katsina wajen bunkasa al’adu da wayar da kan al’umma, Mai Bai wa Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina Shawara na Musamman kan Harkokin Al’adu da Wayar da Kai, Hon. Isa Muhammad Musa Kankara, ya jagoranci tawagarsa zuwa Ma’aikatar Al’adu da Yawon Bude Ido ta Jihar Kano domin karfafa hadin gwiwa tsakanin jihohin biyu.
Ziyarar ta mayar da hankali kan samar da ingantacciyar alaka da musayar kwarewa, tare da tsara hanyoyin hadin gwiwa da za su taimaka wajen farfado da al’adun gargajiya, kare martabar al’adu, da kara wayar da kan al’umma.

A yayin ganawar, Kwamishiniyar Al’adu da Yawon Bude Ido ta Jihar Kano, Hon. Aisha Lawal Saji, ta tarbi tawagar cikin mutunci da karamci, inda ta bayyana farin cikinta bisa wannan ziyarar tare da jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin jihohin Katsina da Kano wajen bunkasa al’adu da yawon bude ido.
A nasa jawabin, Hon. Isa Muhammad Musa Kankara ya bayyana cewa wannan ziyara wani bangare ne na kokarin Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, na farfaɗo da al’adun gargajiya da wayar da kan al’umma. Ya jaddada cewa ofishinsa a shirye yake ya ci gaba da hada hannu da hukumomi da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa al’adunmu sun samu kulawar da ta dace kuma an mika su ga karni masu zuwa.
Ya kuma bayyana cewa hadin gwiwar da aka fara tsakanin jihohin Katsina da Kano zai samar da sabbin dabaru da shirye-shirye da za su kara bunkasa harkokin al’adu, yawon bude ido da wayar da kai.

Tawagar ta samu rakiyar mataimakin Daraktan Al’adu da Wayar da Kai Malam Abubakar Ayuba, da Abdurrahman Ashahabu, tare da sauran jami’an ofishin. Haka kuma, Babban Sakataren Ma’aikatar Al’adu da sauran jami’an gwamnatin Kano sun ba da shawarwari masu amfani domin kara inganta wannan hadin gwiwa.
Wannan ziyara ta sake tabbatar da jajircewar Hon. Isa Muhammad Musa Kankara wajen tabbatar da cewa al’adun gargajiya na Katsina sun ci gaba da bunkasa, tare da amfani da su a matsayin hanyar hadin kai, wayar da kan al’umma da ci gaban jihar.
Allah Ya ci gaba da ba da nasara.
