Gwamna Raɗɗa Ya Rantsar da Sabbin Alƙalan Kotun Ƙolin Shari’a a Katsina
Gwamnan jihar ihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya rantsar da sabbin alƙalan kotun kolin shari’a guda biyu, Kadi Ibrahim Abdullahi Yakubu Ɗandume da Kadi Bala Salisu Daura, inda ya buƙace su da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, adalci da tsoron Allah.
A cewar gwamnan Raɗɗa rantsuwar da suka yi wata amana ce mai girma da za su yi wa Allah da al’umma hisabi a kanta.
Popular News Hausa ta ruwaito cewa sabbin alƙalan sun samu amincewar naɗin su ne bayan hukumar kula da alƙalai ta ƙasa (NJC) ta ba da shawararsu.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa naɗin nasu zai ƙara ƙarfafa tsarin shari’a a jihar tare da haɓaka amincewar jama’a ga kotunan shari’a, yana mai cewa ƙwarewar da suka samu tsawon shekaru za ta taimaka wajen tabbatar da adalci cikin gaggawa ba tare da son rai ba.
Haka kuma gwamnan ya jaddada cewa adalci shi ne ginshiƙin zaman lafiya da ci gaban kowace al’umma, don haka ya buƙaci sabbin alƙalan su yi aiki da riƙon amana, gaskiya da tsoron Allah.
Kazalika ya yaba wa ma’aikatan ɓangaren shari’ar jihar bisa irin gudummawar da suke bayarwa wajen tabbatar da adalci, tare da tabbatar musu da ci gaba da samun goyon bayan gwamnatinsa
Ya kuma yi kira ga dukkan al’ummar jihar Katsina da su haɗa kai wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da ci gaban jihar, yana mai cewa babu wata jiha da ta fi Katsina muhimmanci ga ‘ya’yanta, saboda haka wajibi ne kowa ya ba da tasa gudummawa wajen gina makoma mai kyau ga al’umma.
