Jam’iyyar PDP A Zamfara ta yaba wa babbar kotun Abuja Akan Nasarar jam’iyyar
Daga Hussaini Yero Funtua
Jam’iyyar PDP reshen Jihar Zamfara ta yaba wa kotun tarayya da ke Abuja da tayi masu adalci a hukuncin da ta yanke a Ranar Talata da ta gabata.
Shugaban riko na jihar Hassan Daudawa ne ya yaba Babbar Kotun A tattaunawar sa da manema labarai a hedikwatar Jamiyyar PDP da ke Gusau babban Birnin Jihar Zamfara.
Hassan Daudawa ya bayyana cewa nasarar ta karfafa wa magoya bayan jam’iyyar gwiwa a dukkan matakai.
Sakamakon babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da Samuel Anyanwu ya shigar a ranar Talata, yana neman a tabbatar da shi a matsayin sakataren jam’iyyar PDP na kasa.
Alkalin kotun, Muhammed Umar, ya yi watsi da karar bayan da lauyan Mista Anyanwu ya bayyana cewa wa’adin sakataren jam’iyyar PDP na kasa ya kare a watan Disamba na 2025.
Wadanda aka shigar da kara a matsayin wadanda ake kara a cikin karar sun hada da PDP, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Umar Damagun, shugaban jam’iyyar na kasa; Sunday Udeh ‑ Okoye, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Kudu maso Gabas; Ali Odela, mataimakin sakataren jam’iyyar na Kasa; da Setonji Koshoedo, mataimakin sakataren jam’iyyar na Kasa.
Daudawa ya ce “dukkanmu dole ne mu yi farin ciki da wannan nasara da zata karfafa tsarin gudanarwa na jam’iyyarmu kuma jam’iyyar ta samu cikaken damar tsayawa takara a kowane mukami a babban zaben 2027 mai zuwa.
A cewarsa, dukkan Mukaman cikin jam’iyyar, tun daga Kwamitin Aiki na Kasa (NWC), Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC), Kwamitin Amintattu, da Wakilai na Kasa duk suna nan daram.
Daudawa ya kuma taya hedikwatar jam’iyyar PDP ta Kasa murna tare da tabbatar da biyayyarsu ga shugabancin Shugaban Jam’iyyar na Kasa Kabiru Turaki wanda ya kasance shugaban jam’iyyar na Kasa.
Kuma wannan nasarar ta kada hanta Jam’iyun adawa kuma ta karya lagon masu ficewa daga Jam’iyyar PDP da sunan wai rikici ya tarwatsata .
Akan haka ne Hassan Daudawa yayi kira ga al’ummar Kasar nan da su dawo ma Jamiyyar gaskiya da gaskiya mai kaunar Jama’a da cigaban alumma watau Jamiyyar PDP dan cetosu daga kangin da Jamiyyar APC ta jefasu.
