Malam Kamilu Ɗahiru Gwammaja ya gabatar da nazari a kan yalwar ma’ana ta hanyar tsokaci daga wasu maganganun marigayi Malam Aminu Kano, kuma hakan ne ya kai shi ga kaiwa matakin nasarar kammala Digirin Digirgir wato PhD
Haka kuma yana cikin marubuta littattafan Hausa, tun ana rubutun labarin soyayya, daga baya kuma ya koma yin rubutun littattafai na Ilimi, in da a nan ma ya rubuta littattafai masu yawa.
Daga cikin fitattun littattafan sa akwai Tsanin Hausa na Firamare 1 zuwa 6.
Tsanin Hausa na Junior Secondary na ɗaya zuwa na uku, Jagoran Nazarin Karin Magana da Azabar so da Rabi’atu da kuma sharri takin Masoya da sauran su.
A cikin wani sako da ya wallafa a ranar Alhamis 25 ga Satumba 2025. Dakta Kamilu Ɗahiru Gwammaja, ya bayyana cewa
‘Na samu amincewar malamaina na samun shaidar PhD wato Dr a nazarin harshen Hausa. Godiya ga jagoran gudanar da binciken (Farfesa Isa Mukhtar) da jagoran duba binciken na gida (Farfesa Usman Usaini Fagge) da Shugaban Sashe (Dr Jibril Shu’aibu Adamu) da Jagorar kula da manyan ɗalibai (Farfesa Halima Abdulkadir Dangambo)
Sauran sun haɗa da Mai kula da gabatar da mukaloli (Dr Muhammad Sulaiman Abdullahi) da dukkanin malaman Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya na Jami’ar Bayero ta Kano da Jagoran duba bincike na waje da zaman sahalewa (Farfesa Salisu Garba) daga jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Allah ya saka wa kowa da alheri.
Dakta Kamilu Dahiru Gwammaja ya ce
Jama’a dai da dama ne suke aikawa sakon taya murnar samun wannan babbar nasara da ya yi.