Mata 100 Sun Samu Horo akan Sana’o’i da kuma Daƙile Matsalar Tsoro A Katsina.
Mata 100 Sun Samu Horo akan Sana’o’i da kuma Daƙile Matsalar Tsoro A Katsina.
An yi wa mata 100 bita domin su bada ta su gudunmawa wajen kokarin gwamnatin na magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin arewa baƙi ɗaya.
Taron dai an shirya shi a dakin taro na masaukin baƙi na Shalele da ke Garin Ɗanɗagoro da ke birnin Katsina..

An dai shirya horon ne a ƙarƙashin kulawar baban hafsan sojojin Nijeriya Christopher Musa domin su kasance sun bada ta so gudunmawar wajen maganin matsalar tsaro.
Kamar yadda Babban kodinata mai kula wayar da kan jama’a bisa sahalewar baban hafsan sojojin Nijeriya Malam Lawal BK ya bayyana cewa an zaɓo kungiyoyin mata ne daga shiyyar Katsina domin a ba su horo akan sana’o’i

Kuma haka na da nufin baiwa mata dama su bada ta su gudunmawar wajen ganin an daƙile ayyukan ta’addanci a jihar Katsina da arewacin Nijeriya baƙi ɗaya
Ya ƙara da cewa da yawan lokuta ana amfani da mata wajen kaiwa ‘yan bindiga makamai da kwayoyi wani lokaci ba tare da sun sani ko kuma illar yin haka.

A cewar sa, ofishin baban hafsan sojojin Nijeriya Christopher Musa ya taɓa shirya irin wannan bitar akan matan sojojin da suka rasa ran su a fagen daga yanzu kuma sun shiryawa kungiyoyin mata
Masana dai sun bada horo a fanni daban-daban akan mahimmanci yin sana’a ga mata tare da koya masu yadda ake yin sana’a ba tare da sun biya ko sisi ba.

Kazalika hakan na da nufin jawo hankalin mata da su kauracewa duk wani aiki da zai iya jefa su wajen taimakawa ‘yan bindiga masu kashe al’umma sun kaurace masa

Lawal BK wanda ya ce sun bi hanya mafi dacewa wajen zaɓen waɗannan matan, kuma za su cigaba da wayar da kan mata domin a cewar sa ta haka ne za a toshe hanyoyin da ɓarayin daji ke bi domin comma manufar su
Sana’o’in da ake koyar da matan sun haɗa da yin sabili da turaren kanshi da kuma takalma da sauransu domin su kasance masu dogaro da kan su.

A ƙarshen taron dai an rabawa matan shaidar halartar wannan bita ta wuni guda akan sana’o’i da kuma gujewa fadawa aikin ta’addanci da mafi yawan mata ke shiga ba tare da sun sani ba.
