Mauludin Jihar Katsina Karo Na 27: An Fayyace Wajibcin Girmama Annabi S.A.W
Taron Mauludin jiha da aka saba gabatarwa duk shekara, a bana ma an gudanar da shi a ƙaramar Hukumar Bindawa da ke shiyyar Daura a jihar Katsina karo na 27
Taken Taron Mauludin na wannan shekara shi ne, wajibcin girmama Annabi Muhammad S.A.W da kuma irin maganar da ta da ce a jingina masa

Bayan buɗe taron da addu’o’i na musamman domin neman albarka sai manyan Malaman da aka tsare za su gudanar da jawabai akan batutuwa guda biyu wato yadda ake girmama Annabi A.S.W da kuma irin maganar da ta da ce a jingina masa suka fara aikin su.
Shehunai guda biyu aka ba dama domin yi wa wannan muhimmanci ɓangare adalci ta hanyar yin amfani da hikima domin isar da wannan sako inda Sheikh Attahir Imam Katsina da Malam Ibrahim S Fawa Bindawa suka gabatar.

Waɗannan Malamai sun yi ruwan gwala-gwalai jawabai masu nuna irin girma da daraja ta fiyayyan halitta Annabi Muhammad S A.W.
Ko bayan haka shehunai sun yi bayani dalla-dalla akan halin da al’umma ta samu kanta na taɓarɓarewar tarbiyya inda anan suka yi ƙarin haske da kuma irin matakan da ya kamata a dauka domin dawowa al’umma cikin hayyacin ta.

Kamar yadda aka sani wannan taron Mauludi ana shirya shi ne ƙarƙashin jagorancin Munazzamatu Fiyyanil Islam reshen jihar Katsina tare da majalisar shura ta Malaman zaure.
Kamar yadda aka saba kowace shekara Kwamitin gudanar da Mauludi na zabar wata Karamar hukuma daga cikin shiyya uku na Katsina, Daura da Funtua domin gudanar da wannan gagarumin taro, a wannan shekara an zabi ƙaramar hukumar Bindawa da ke shiyyar Daura dan gudanar da wannan muhimmin taro.

Taron ya samu halartar manyan Shehunai, Malamai da Muƙaddamai daga ciki da wajen jihar Katsina. Inda Malamai da shugabanni daga ɓangarori daban-daban kamar shugaban Muzamma na jihar Katsina Sheikh Ishak Nuhu Ɓatagarawa da Sheikh Hadi Balarabe da duk sun gabatar da jawabai
Kazalika shugaban Muzzamatu Fityanil Islam na Ƙasa Shiekh Alhaji Malam Mahmud Salga Kano yayi jan hankali da addu’ar samun zaman lafia da cigaban jihar Katsina da Ƙasa baƙi ɗaya. inda wakilan Sheikh Tijjani Bala Kalarawi, Imam Muhammad Nasir Adam Kano da Malam Nasidi Goron Dutse sukayi bayanai a mamadinsu ɗaya bayan ɗaya.

Manyan masu masauki baƙi sun haɗa da shugabannin ƙananan hukumomin Mani da Bindawa Hon. Badaru Musa da Hon. Muhammad Yunusa Bagiwa tare da hakiman Doro da Bindawa
Tawagar Mu’assatil Khairiyya na daga cikin waɗanda suka halarci wannan babban taro ƙarƙashin jagorancin Hajiya Hauwa Umar Raɗɗa

Daga ɓangaren gwamnatin jihar Katsina kuwa an samu halartar Sakataren gwamnati Barista Abdullahi Garba Faskari wanda ya wakilci gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa da kwamishinan ma’aikatar harkokin Addinai Hon. Ishaq Shehu Dabai
Sauran sun haɗa da mai taimakawa gwamna na musamman akan harkokin Ɗarika Malam Mahi Bello da jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa masu ruwa da tsaki da sauran al’umma

Daga ƙarshe Sheikh Ɗayyabu Imam Katsina da Sheikh Mansur Kofar arewa Daura da Imam Abdurrahaman Funtua suka jagoranci gabatar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya a jihar Katsina da arewacin Nijeriya baƙi ɗaya
